NIJERIYA
3 minti karatu
Yadda ‘yan wasu Nijeriya suka yi kashin ƙulli 116 na heroin da hodar ibilis a gaban jami’an NDLEA
Mutumin da ake zargi da safarar hodar ibilis ya ce ya shafe fiye da awa biyu yana ƙoƙarin tura ɗauri tara na hodar ibilis a cikin duburarsa.
Yadda ‘yan wasu Nijeriya suka yi kashin ƙulli 116 na heroin da hodar ibilis a gaban jami’an NDLEA
Kusan kowane mako hukumar NDLEA na bayar da rohotannin kama masu safarar ƙwayoyi / NDLEA
6 awanni baya

Wasu mutum biyu ‘yan Nijeriya waɗanda suka dawo daga ƙasar Brazil sun yi kashin ƙulli 116 na heroin da hodar ibilis bayan sun shafe kwanaki a tsare a hannun jami’an hukumar yaƙi da sha da miyagun ƙwayoyi NDLEA a filin jirgin Murtala Muhammed na Legas.

Hukumar ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, mai suna Ofoma Sunday, mai shekara 46, an kama shi a ranar Talata, 16 ga Satumbar 2025, a Terminal 2 na filin jirgin saman Legas bayan isowarsa daga Laos, Brazil, ta jirgin Ethiopian Airlines.

“An kai shi gwajin hoton jiki wanda ya tabbatar da ya haɗiye miyagun ƙwayoyi. Ofoma ya bar Nijeriya zuwa Brazil a ranar 3 ga Satumba domin kawo kayan zuwa Legas don karɓar ladar dala $2,500 idan ya kammala isar da su cikin nasara.

“Nan da nan aka kai farmaki a Otal ɗin Eliata da ke unguwar Amuwo Odofin a Legas, inda aka umarce shi ya gana da Nweke Jude Chuckwudi, wanda aka tura domin sa ido kan fitar ƙwayoyin daga cikinsa a otal ɗin da kuma tattarawa.

“An kama Nweke mai shekara 55 a lokacin. Jimillar kwayoyi 111 na heroin masu nauyin kilo 1,452 Ofoma ya fitar ta hanyar bayan gida da ya yi sau takwas, ji sanarwar kakakin hukumar, Femi Babafemi.

Haka kuma NDLEA ta bayyana cewa wani da ya dawo daga Brazil mai suna Ukachukwu Frank Ikechukwu, an kama shi a filin jirgin saman Legas yayin tantance fasinjojin jirgin Ethiopian Airlines wanda ya taho daga Brazil sannan ya biyo ta Addis Ababa a ranar Juma’a, 19 ga Satumba.

A cewar hukumar, an kai shi gwajin hoton jiki wanda ya tabbatar da ya haɗiye miyagun ƙwayoyi, sannan yayin da aka sa ido a kansa domin yin kashinsu, ya kasaye ƙulli biyar da hodar ibilis da nauyinsu ya kai gram 145.

 “A cikin bayaninsa, ya amsa cewa ya sayi ƙwayoyi tara na wannan muguwar kwaya a Brazil ya kuma tura su gaba ɗaya cikin duburarsa, wani tsari da ya ce ya dauki kusan awa biyu.

A bayanin da ya yi wa hukumar, ya sayi ɗauri tara na ƙwayoyin ne a Brazil kuma ya shafe fiye da awa biyu yana ƙoƙarin tura su a cikin duburarsa.

A lokacin da suka isa Addis Ababa, sai ya fara jin zafi a dubararsa wanda hakan ya sa ya yanke shawarar cire kwayoyin daga jikinsa.

Ya ce sakamakon saurin da yake yi na samun jirgin da zai tafi Nijeriya, ƙulli bakwai kawai ya iya mayarwa a cikin duburar tasa, inda ya zubar da sauran a cikin ban-ɗaki.

Sannan kuma a lokacin da yake cikin jirgi zuwa Nijeriya ya ƙara samun rashin sukuni inda ya shiga ban-ɗaki ya ƙara cire wasu ƙulli biyu, inda ya rage saura biyar, waɗanda kuma aka kama shi da su.