Gwamnatin Jihar Enugu da ke kudancin Nijeriya ta yi alƙawarin bayar da tukwuicin naira miliyan goma ga duk mutumin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargi da kashe fitaccen limamin cocin Katolika Matthew Eya.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Enugu, Malachy Agbo, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun yi masa kwanton-ɓauna sannan suka harbe shi a yayin da yake kan hanyar komawa gida daga Birnin Enugu Urban. Limamin cocin mamba ne na Cocin Nsukka Catholic Diocese, wadda ta tabbatar da kisansa.
A sanarwar da Mr Agbo ya fitar, ya ambato gwamnatin Enugu tana “yin Allah wadai da kakkausar muryar” bisa “mummunan kisan” da aka yi wa limanin cocin.
“Gwamnatin Enugu tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan limanin cocin, da Catholic Diocese ta Nsukka, da kuma mabiya ɗarikar Katolika baki ɗaya bisa wannan iftila’i,” a cewar kwamishinan.
Ya bayyana makasan a matsayin “matsorata” waɗanda suka aiwatar da kisan “rashin imani”, inda ya sha alwashin cewa gwamnati za ta kama ‘yan bindigar da suka yi wannan aika-aika.