24 Satumba 2025
Hukumar Kula da Layin Dogo ta Nijeriya, NRC ta fitar da sakamakon binciken da ta gudanar kan hatsarin da jirgin ƙsan Abuja-Kaduna ya yi a kwanaki baya.
A sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Shugaban NRC, Kayode Opeifa, hukumar ta ce sakamakon binciken ya nuna cewa tsananin gudu da matuƙin ke yi da kuma rashin iya sarrafa birkin jirgin ne suka jawo faɗuwar da ya yi.
NRC ta alaƙanta hakan da cewa kura-kurai ne irin na ɗan’adam.
Za ku so karanta wadannan
Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya gabatar.
A ranar 26 ga watan Agustan da ya wuce ne jirgin ƙsan mai ɗauke da fasinjoji 618 ya kauce daga hanyarsa tare da faɗuwa inda har mutum 21 suka ji raunuka.
Lamarin ya faru ne a garin Asham da ke kusa da Jere.