NIJERIYA
4 minti karatu
UNGA 80: Abubuwa biyar da Kashim Shettima ya faɗa a zauren MDD
Ya ce MDD za ta sake samun ƙimarta ne kawai idan ta nuna yadda duniya take a halin yanzu, ba yadda take a da can ba.
UNGA 80: Abubuwa biyar da Kashim Shettima ya faɗa a zauren MDD
Shettima: Samar da ƙasashe biyu ita ce mafita ga Falasɗinu / Nigeria Presidency
25 Satumba 2025

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya yi jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) inda ya yi magana kan batutuwa ciki har da na Falaɗinu da kuma samar wa Nijeriya kiujerar dindindin a kwamitin tsaro na MDD.

 “Dole Nijeriya ta samu kujera ta dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD. Ya kamata a yi wannan a wani ɓangare na garambawul wa ɓangarori [na MDD},” a cewar mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya.

Ya ce MDD za ta sake samun kimarta ne kawai idan ta nuna yadda duniya take a halin yanzu, ba yadda take a da can ba

Kwamitin tsaro

Ya ƙara da cewa a lokacin da aka kafa MDD Nijeriya ƙasa ce mai mutum miliyan 20 da ake yi wa mulkin mallaka kuma ba ta samu wakilci a teburin majalisar inda aka ɗauki matakai kan makomarta ba.

“A yanzu mu ƙasa ce mai cin gashin kanta da sama da mutum miliyan 236, wadda ake kiyasin za ta zama ƙasa ta uku a yawan jama’a a duniya wadda take ɗaya daga cikin ƙasashe mai mutane mafi ƙarancin shekaru a duniya,” in ji Shettima.

Baya ga haka, Nijeriya ƙasa ce mai tabbatar da zaman lafiyar a yanki tare da kasancewa ƙasa da ta daɗe tana ba da gudumawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

“Batunmu na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD, buƙata ce ta adalci da wakilci da garambawul da zai dawo da yarda wa a majalisar wadda akanta ne hadin kan duniya ta rataya,” in Shettima.

Magana kan Falasɗinu da harin Qatar

Ɗaya daga cikin ababen da ya mayar da hankali kai a jawabinsa shi ne tashin hankalin da ake a Gaza da kuma harin tsokana da aka kai kan Qatar. Shettima ya ce ba wai saboda tsagoran rashin hukunta waɗannan matakan ne kawai Nijeriya take magana kansu ba, sai dai saboda sanin da ƙasar ta yi cewa irin waɗannan hare-haren ba sa ƙarewa a inda aka fara su.

“Bai kamata mutanen Falasɗinu su kasance waɗanda harin tsautsayi zai yi kasanu ba wajen neman maslahar wasu. Mutane ne, waɗanda kimarsu ya yi daidai da namu kuma sun cancanci irin ‘yanci da mutunci da dukkanmu muka saba da su,” in ji Shettima.

Yafe basussuka

Shettima ya ce duk da cewa Nijeriya da ma Afirka ta daidaita lamurra a cikin gida, suna buƙatar yafe basussuka.

“Muna buƙatar mataki na gaggawa domin yafe basussuka- ba wai a matsayin sadaka ba amma a wata hanya ga zaman lafiya da wadata da za ta amafani ga dukkanmu gabaɗaya,” in ji shi.

“Ina kira da a samar da wani sabon tsari da zai kuka da basusuukan ƙasashe, wani abu kaman kotun duniya na kuɗi, wanda zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar kuɓucewa daga tsarin tattain arziƙi na sayar da kayayyakin da ba a inganta ba,” a cewar Shettima.

Ya ce: “Muna buƙatar mataki na gaggawa na ƙarfafa yafe basusuuka da kuma samar da kuɗi.”

Amfana da ma’adinai

Daya daga cikin ababuwan da Shettima ya faɗa shi ne: “Ƙasashe masu arziƙin ma’adinai dole su amfana daga waɗannan ma’adinan.”

Ya ce tarihi ya nuna a Nijeriya cewa idan al’ummomin da ke inda ake samar da ma’adinai ba sa amfana da ma’adinan ba za a samun zaman lafiya ba.

“Saka jari wajen nema da inganta waɗannan ma’adinan a Afirka zai ruɓanya hanyar samar da ma’adinai ga kasuwar duniya da rage tashin hankali tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi.

“Zai kuma taimaka wajen tsara zaman lafiya da wadata a wata nahiyar da sau da yawa aka bari a baya yayin da ake tsere tsakanin ɓangarori,” in ji shi.

Ci-gaban ƙirƙirarriyar basira

Game da ƙirƙirarraiyar basira, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce fasahar tana tattare da ƙalubale mai yawa da ya kamata a magance su musamman ga ƙasashen Afirka.

“Dole mu cike giɓin ci-gaba na fasahar sadarwa. Kamar yadda abokinmu Babban Sakatare ya ce: dole ‘A.I.’ ya zaman wakilin ‘Afirka na Ciki’”, inji Shettima.

Ya ce ya kamata duniya ta yi amfani da damarmakin da fasaha ta samar da kuma samar da linzamin da ya kamata a samar masa domin inganta ci-gaba tare da hana ta’adin da zai iya haddasawa.

Ya ce abin ya da fi tayar masa da hankali shi ne matasa masu tasowa waɗanda ba su da yarda domin ba za su yarda da komai ba.