Aƙalla mutum 13 sun rasu a Nijeriya sakamakon ruftawar wani ramin haƙar ma’adinai da ke Kadauri a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da ƙananan masu aikin haƙar ma’adinai suke aiki a ƙarƙashin ƙasa.
Wasu majiyoyi sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa an gano gawawwakin mutum 13 a ƙarƙashin ɓaruguzai inda har yanzu akwai wasu da dama da suka maƙale.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Hukumar Kula da Albarkatu ta Jihar Zamfara Nasiru Bamanga ya tabbatar da faruwar lamarin mummunan lamarin sai dai ba shi da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru.
“Na ji labarin faruwar lamarin, sai dai ban samu cikakkun bayanai ba. Zan tafi wurin can anjima Insha Allahu, sannan zan ba ku cikakken bayani bayan na dawo,” kamar yadda Bamanga ya shaida wa gidan talabijin ɗin.
Wuraren haƙar ma’adinai da ke Kadauri a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara sun yi ƙaurin suna wurin zama sanadin asarar rayukan mutane musamman masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.