NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kama masu aikata laifuka 120 ciki har da masu taimaka wa ‘yan ta’adda 26
A arewa maso gabashin Nijeriya, dakarun Operation Hadin Kai sun kuɓutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su kuma suka kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda 26  tare da kashe mayaƙan Boko Haram a Jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Sojojin Nijeriya sun kama masu aikata laifuka 120 ciki har da masu taimaka wa ‘yan ta’adda 26
Nijeriya na fama da matsalar tsaro daga 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane / Reuters
26 Satumba 2025

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta ce dakarunta sun kama masu aikata laifuka fiye da 120 ciki har da mutum 26 da ke taimaka wa ‘yan ta’adda, sannan sun kuɓutar da mutane 41 da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar tsakanin 14 zuwa 22 ga watan Satumba.

Daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Manjo Janar Markus Kangye, ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Alhamis cewa dakarunsu sun gudanar da waɗannan ayyuka ne a dukkan fagage daga — a arewa maso gabas, arewa maso yamma, arewa maso tsakiya, kudu maso kudu da kuma kudu maso gabashin Nijeriya.

A arewa maso gabashin Nijeriya, dakarun Operation Hadin Kai sun kuɓutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su kuma suka kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda 26  tare da kashe mayaƙan Boko Haram a Jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Dakarun Operation Fansan Yamma kuma a arewa maso yammacin Nijeriya sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ‘yan ta’adda a jihohi biyar kana suka kama ƙasurgumin mai aikata laifuka mai suna Mallam Abubakar Ahmadu da abokana aikinsa shida.

A arewa maso tsakiyar Nijeriya kuwa, dakarun Operation Enduring Peace sun kama mutum 52 da ake zargi da aikata laifuka a jihohin Filato da Kaduna yayin da suka kuɓutar da mutum tara da aka yi garkuwa da su.

Dakarun Operation Whirl Stroke kuwa sun ‘yanta mutum takwas a jihohin Benue da Taraba da Kogi da Nasarawa da kuma Birnin Tarayya Abuja, inda suka kuma wani babban mai garkuwa da mutane mai suna Saawuan Wuaiyolna.

A yankin Kudu maso kudancin Nijeriya, dakarun Operation Delta Safe sun lalata wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba guda 16 tare da hana satar mai da darajarsa ta kai naira miliyan 19.75, kuma suka kama mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka da kuma kuɓutar da mutum biyar da aka yi garkuwa da su.

Dakarun Operation Udo Ka kuwa a kudu maso gabashin Nijeriya sun ‘yanta mutum uku da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato makamai da bamabamai.

Manjo Janar Kangye ya yaba wa dakarun bisa jajircewar su da ƙwarewarsu, yana mai kira ga jama’a su ci gaba da taimaka wa sojojin da bayanai a kan lokaci.