Gwamnatocin Jihohin Ondo da Kogi da ke Nijeriya sun yi kira ga mutane su kwantar da hankulansu game da wasu bayanan sirri na hukumar tsaron farin kaya (DSS) kan yiwuwar ƙaddamar da hare-haren ta’addanci na ƙungiyar ISWAP a wasu yankunan jihohin.
Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na Jihar Ondo, Idowu Ajanaku, yayin da yake bayani ga manema labarai ranar Laraba ya ce bayanan sirrin na yau da kullum ne waɗanda hukumomin tsaro ke bai wa gwamnatocin jihohi, yana mai ƙarawa da cewa ana amfani da bayanan ne domin auna barazana ga tsaro da kuma ɗaukar matakan magance su.
Ajanaku ya ba da tabbacin cewa gwamnati da hukumomin tsaro sun riga sun fara aiki a kan bayanan sirrin inda ake ɗaukar matakai domin tabbatar da tsaron jama’a, kamar yadda jaridar The Guardian ta Nijeriya ta ruwaito.
Kazalika, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Olayinka Ayanlade, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce rundunar ta ƙaddamar da kayayyakin aiki da na tattara bayanai domin daƙile matsalar da wuri.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa gwamnatin jihar Kogi ta yi kira ga mazauna jihar su kwantar da hankulansu su kuma sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a yankunansu.
A wata sanarwa da kwamishinan watsa labaran jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar gwamnatin jihar ta bayyana bayanan sirrin a matsayin wani mataki na cim ma nasara, tana mai cewa wannan ya nuna irin yadda hukumar DSS take aiki a kan lokaci kuma sauran hukumomin tsaro suke aiki wajen kare ‘yan Nijeriya.
Kwamishinan ya tabbatar wa ‘yan jihar cewa gwamnatin Jihar Kogi tana aiki tare da hukumar DSS da rundunar sojin Nijeriya da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa sun daƙile duk wani harin ‘yan ta’adda kafin ya yi barazana ga rayuka da ƙadarori.










