Na san duk iyaye suna son ’ya’yansu su zama masu kaifin basira da hikima, ta yadda damarsu ta yin nasara a rayuwa za ta inganta.
Abubuwa ne da ya yawa suke taimakawa wajen bunƙasa ƙwaƙwalwa da kaifin basirar yara da hikimarsu.
Kaifin ƙwaƙwalwar yara da basirarsu tana samuwa ne a matakai daban-daban na rayuwarsu, tun daga ɗaukar cikinsu har zuwa girmansu.
Sannan akwai abubuwa da dama da suke taimakawa wajen samun ’ya’ya masu basira, ciki har da abinci mai gina-jiki, da kulawar da yara ke samu, da kuma soyayyar da iyaye suke nuna musu, har ma da wajen da suka taso.
Wannan ne bayanin da masana da ƙwararru kan lafiyar ƙwaƙwalwa suke faɗa, kamar yadda wani likitan ƙwaƙwalwa, Dokta Aliyu Muhammad da ke aiki da Asibitin Ƙwaƙwalwa na Barnawa da ke Jihar Kaduna a Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika.
Za mu taƙaita bayani kan nau’ukan abinci da ke taimaka wa ƙwaƙwalwar yara ƙanana, ’yan-wata shida zuwa akalla shekara shida.
Mun fara daga bayan wata shida ne, saboda watanni farko na haihuwar yaro zuwa wata shida, nonon-uwa zalla jariri ke buƙata, kamar yadda masana harkokin lafiya ke yawan faɗa.
Nonon uwa ya ƙunshi duka abubuwan da jariri ke nema don gina garkuwar jiki, da kuzari, da girma har tsawon watanni shida.
Haka ne ya sa jariri ba ya bukatar wani abin-sha, hatta ruwa, jus, zuma, ko abinci mai laushi. Duka wadannan za su iya cutar da tumbin jariri ko janyo masa gudawa da pneumonia, in ji ƙwararru.
Madogara bincike
Cibiyar Lafiya ta Jami’ar California da ke kasar Amurka, ta bayyana cewa ana fara gina tubalan kaifin ƙwaƙwalwar yara ne tun kafin su fara magana da tafiya, kuma bincike ya tabbatar da cewa wasu nau’ukan abinci suna taimakawa wajen samun hakan.
Haka nan, cibiyar ta ce idan aka yi rashin sa’a yara ƙanana ba su samu wasu mhimman sinadarai ba daga abinci da suke ci, to hakan zai iya rage kaifin ƙwaƙwalwarsu, da kaifin haddarsu, da kuma ƙoƙarinsu a makaranta.
Wato dai, rashin bai wa yaro abinci mai gina jiki, ko tamowa na jawo rage girman yara, da rage kaifin ƙwaƙwalwarsu, da ma kuzarinsu.
Yanzu za mu duba nau’in abinci biyar da ya kamata a riƙa ba yara idan sun cika wata shida, wadanda za su taimaki kaifin ƙwaƙwalwarsu da gina jikinsu, kuma abubuwa ne da duk da halin matsin da ake ciki a ƙasashenmu na Afirka, ba su fi ƙarfin talaka ba saboda rangwame da sauƙin samun su.
Ge jerin abincin da aka tabbatar suna inganta kaifin ƙwaƙwalwa
1. Wake
Farko dai shi ne wake. E, wake dai fari, ko ja, ko kuma waken soya da muka sani, duka suna da mahimmanci sosai wajen bunƙasa kaifin ƙwaƙwalwa, kamar yadda cibiyar binciken ta bayyana.
Wake yana dauke da sinadarai masu yawa da suke taimaka wa ƙwaƙwalwar yara, ciki har da Zinc da Protein da Iron da Folate da kuma Choline. Shi ma waken soya yana dauke da mahimmin sinadarin nan da ke ƙara kaifin ƙwaƙwalwar yara, wato Omega-3 Fatty Acids, kamar yadda cibiyar ta bayyana.
2. Ƙwai
Abinci na biyu mai bunƙasa kaifin kwakwalwa ƙwaƙwalwar yara shi ne ƙwai. Ƙwai ya ƙunshi sinadarai kamar Choline, da Vitamin B12 da kuma Protein, kamar yadda wani masanin kimiyyar abinci, Malam Buhari Musa Yusuf ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
3. Gyaɗa
Abinci na uku mai ƙara basirar yara shi ne gyaɗa, a cewar Malam Buhari, wanda yake koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna (wato Kaduna Polytechnic).
Ga misali, kunun gyaɗa wanda ake yi daga gyaɗa yana ƙunshe da mahimman sinadarai kamar Zinc da Protein, kuma kamar wake, waɗanda ke taimakawa wajen bunƙasa kaifin ƙwaƙwalwa.
4. Gero
Abin na hudu shi ne nau’ukan gero, wato gero, ko maiwa, ko dauro, ko jan gero, wanda hatsi ne da idan an sarrafa shi ya zama gari, yakan taimaka wa yara a fannin gina jiki, sama da sauran hatsi, kamar yadda hukumar FAO ta bayyana.
Gero na ƙunshe da sinadaran zinc, niacin, vitamin B6, folic acid, magnesium, da phosphorus, kuma ba shi da sinadarin gluten cikinsa irin na sauran hatsi.
Dokta Muhammad Baba Bello, wani masani kan aikin gona wanda yake da ƙwarewa a yankin Afirka ta Yamma, kuma yake koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce gero hatsi ne da ke taimaka wa wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a Afirka, musamman a yankunan karkara.
5. Kayan ganye
Abinci na biyar da yake taimakon yara ƙanana su samu ƙwaƙwalwa mai kaifi shi ne ganyayyaki, kamar alayyahu, zogale, da ugu, da sauransu.
Irin wadannan ganyayyaki sun ƙunshi sinadarin Zinc da Iron. Kuma cibiyar lafiya ta Jami’ar ta California da ke Amurka, ta ce sinadaran suna cikin jerin sinadaran da idan aka rasa su ake ganin matsala wajen a ƙwaƙwalwar yara ta fuskar rashin ƙoƙarinsu a makaranta da kuma hazaƙarsu a fafutukar duniya.
Kamar yadda muka bayyana a farko, duka wadannan na’ukan abinci ba masu tsada ba ne da za a ce sun gagari talaka.
Tsafta da bi a sannu
Masana harkokin lafiya sun ce wani abin lura shi ne, lokacin da jariri ya cika watannin shida kuma za a fara gwada ba shi abinci, to yana da kyau a kula wajen fara ba shi abinci mai ruwa-ruwa mai ƙunshe da sinadaran gina-jiki.
Za a iya farawa da kunu, da abinci mai laushi da aka yi da gyada, wake, gero, ƙwai, da ganyayyakin da aka niƙa.
Kuma kada a manta, idan hali ya samu, ana iya ƙara wa da jajjagen nama ko kifi, da ‘ya’yan itace kamar ayaba, mangwaro, gwanda, da kabewa, saboda su ma suna da mahimmiyar rawa wajen gina jiki da ƙara basirar yara.
Bugu da ƙari, ya wajaba a kula wajen haɗa abincin cikin tsafta saboda guje wa cuta, sannan a wanke hannu da sabulu kafin haɗa abinci.
Sannan a sani cewa, yara sukan bambanta wajen karbar abinci baya ga nonon-uwa, haka ma wajen karbar nau’ukan abinci, inda wasu yaran kan dauki lokaci mai tsawo kafin sabawa da wani abincin kafin wani.
A bi a sannu tare da ƙarfafa gwiwar yaro don ya ci abinci, tare da sassaɓawa a nau’ukan abincin. Wato sai a ringa sauya wa yaro abinci, sannan a ringa sauya kauri da yawan abincin, har yaro ya fara cin abinci daidai da na manya.
Amma dai a kula, a daina cika wa yara ciki da abinci marasa gina-jiki kamar taliyar yara wato noodle, ko farar shinkafa, ko zallan koko.

















