Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a yi ruwan sama ai ƙarfi da tsawa daga ranar Litinin zuwa ranar Laraba a faɗin ƙasar.
Hukumar, a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, ta bayyana cewa za a yi tsawa da ruwa a jihohin arewacin Nijeriya ciki har da Jigawa da Zamfara da Kano da Kaduna da Bauchi da Yobe da kuma Katsina, farawa daga safiyar Litinin, inda ake tsammanin ruwan da za a yi da rana zai kai jihohin Kebbi da Adamawa da kuma Taraba.
“Za a iya samun ambaliya a jihohin Bauchi da Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma Kano a wannan lokacin,” in ji sanarwar.
“Jihohin tsakiyar Nijeriya da suka haɗa da Neja da Benuwe da Birnin Tarayya Abuja da Filato da kuma Nasarawa za su fuskanci hadari da ruwan sama da safiya da babbar barazanar ambaliya a wasu yankunan Filato.
“A kudu kuwa yayyafi zuwa matsakaicin ruwa za a yi a jihohin Ondo da Imo da Abia da Enugu da Ebonyi da Anambra da Edo da Delta da Bayelsa da Ribas da Cross River da kuma Akwa Ibom,” in ji NiMet .
Hukumar ta ce ranar Talata za a rana da hadari a arewa, yayin da ake hasashin za a yi tsawa da ruwa a wasu yankunan jihohin Adamawa da Taraba da wasu jihohi maƙwabta.
“Yankunan tsakiya da kudancin ƙasar za su ci gaba da fuskantar matsakaicin ruwan sama.
“Zuwa ranar Laraba, jihohin arewaci ƙasar za su fuskanci safiya mai rana da inda za a yi tsawa da ruwan sama daga baya, yayin da yankin tsakiyar ƙasar zai fuskanci hadari da matsakaicin ruwan sama.
“Jihohin kudanci, ciki har da jihohin Ebonyi da Akwa Ibom da Ribas da kuma Cross River, za su fuskanci ruwan sama na safiya da kuma matsakaici zuwa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da rana,” in ji hukumar.
NiMet ta yi gargaɗi mazauna wuraren da ake iya samun ambaliya cewa su tayar da matakan bayar da taimakon gaggawa kuma su guji tuƙi cikin ruwan sama mai ƙarfi tare da ɗaure duk wani abin da ke a kunce da kuma shirya wa iska mai ƙarfi da sanyin cikin dare
“An buƙaci kamfanonin jiragen sama su samu rahotannin yanayi na filayen jiragen sama domin su iya shiryawa lamarin,” in ji hukumar










