NIJERIYA
3 minti karatu
‘Yan sandan INTERPOL sun kama ‘manyan mambobin ƙungiyoyin ta’addanci’ 11 a Nijeriya
An gudanar da wannan kame ne a wani samame mai laƙabin Operation  Catalyst, wani gagarumin aiki da aka tsara domin yakar masu ɗaukar nauyin ta’addanci da sauran ayyukan laifuka masu alaƙa da su a ƙasashe shida na Afirka.
‘Yan sandan INTERPOL sun kama ‘manyan mambobin ƙungiyoyin ta’addanci’ 11 a Nijeriya
Ƙasashen da suka shiga aikin sun haɗa da Nijeriya, Angola, Kamaru, Kenya, Namibiya, da Sudan ta Kudu.
16 awanni baya

Hukumar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa wato INTERPOL ta ce an kama mutum 11 waɗanda ake zargi manyan mambobi ne na ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya.

An gudanar da wannan kame ne a wani samame mai laƙabin Operation  Catalyst, wani gagarumin aiki da aka tsara domin yakar masu ɗaukar nauyin ta’addanci da sauran ayyukan laifuka masu alaƙa da su a ƙasashe shida na Afirka.

A cewar INTERPOL, aikin ya ɗauki watanni uku — daga Yuli zuwa Satumban 2025 — kuma ya an kama mutum 83 tare da gano mutane 160 da ake zargi da hannu a irin waɗannan laifuka.

Ƙasashen da suka shiga aikin sun haɗa da Nijeriya, Angola, Kamaru, Kenya, Namibiya, da Sudan ta Kudu.

A Nijeriya, INTERPOL ta tabbatar da cewa an kama wasu mutum 11 da ake zargi da ta’addanci, ciki har da manyan mambobin wasu ƙungiyoyin ta’addanci daban-daban.

Aikin ya kuma gano wasu hanyoyin kuɗi da ake zargin suna tallafa wa ayyukan ta’addanci ta hanyar mu’amaloli ba bisa ƙa’ida ba da kuma damfara ta yanar gizo.

INTERPOL ta ce jami’an tsaro sun tantance mutane da kungiyoyi fiye da 15,000, kuma sun gano kuɗaɗe kimanin dala miliyan 260 a kudaden da ake amfani da su kai tsaye da kuma na yanar gizo da suka shafi kuɗaɗen ta’addanci.

An riga an kwace kimanin dala 600,000 yayin da bincike ke ci gaba don ganowa da dawo da wasu kadarori.

Aikin ya kuma gano damfara ta kudi, zamba ta yanar gizo, halarta kuɗin haram, da kuma amfani da kuɗaɗen yanar gizo wajen tallafa wa ta’addanci.

An gudanar da aikin tsakanin INTERPOL da Ƙungiyar Haɗin Kan ‘Yan Sanda ta Afirka (AFRIPOL).

Sakataren Janar na INTERPOL, Valdecy Urquiza, ya ce wannan haɗin gwiwa na da muhimmanci wajen fatattakar hanyoyin da ke tallafa wa ta’addanci.

Shi ma Daraktan AFRIPOL, Ambasada Jalel Chelba, ya yaba da nasarar aikin, yana cewa hakan hujja kan ce cewa Afirka ta haɗu wuri ɗaya wajen yaki da ta’addanci.

INTERPOL ta ƙara da bayyana cewa a Angola, hukumomi sun kama mutane 25 tare da kwace dala 588,000, wayoyi 100 da kwamfutoci 40 a wani bincike makamancin haka.

A Kenya, ‘yan sanda sun rushe wani hanyar wanke halasta kuɗaɗen haram ta da darajarsu ta kai dala 430,000, da ake zargin suna da alaƙa da ta’addanci, inda aka kama mutane biyu.

A wani lamari na daban a Kenya, an kama wasu mutum biyu da ake zargin suna amfani da kuɗaɗen yanar gizo wajen jawo matasa su shiga ƙungiyoyin ta’addanci a gabashi da arewacin Afirka.