NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 150 da suka maƙale a birnin Agadez na Nijar
Rukunin mutanen da suka koma ya ƙunshi maza manya 88 da mata manya 32, yara maza 14 da kuma yara mata 16, inda suka koma Nijeriya ƙarƙashin shirin Assisted Voluntary Return — wato shirin nan na taimaka wa masu son komawa ƙasashensu bisa raɗin kansu.
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 150 da suka maƙale a birnin Agadez na Nijar
Bayan an kammala rajista, an kai su masauki a ranar 24 ga Oktoban, 2025 domin ci gaba da tantance su. / NEMA
11 awanni baya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta karɓi ‘yan Nijeriya 150 da suka dawo daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin shirin Assisted Voluntary Return (AVR) — wato shirin nan na taimaka wa masu son komawa ƙasashensu bisa raɗin kansu.

Mutanen sun iso filin jirgin sama na Aminu Kano da misalin ƙarfe 5:20 na Asubahin ranar Alhamis, 23 ga Oktoban 2025 a cikin wani jirgi wanda aka yi shatarsa wanda ofishin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa reshen Jihar Kano ya tsara.

An gudanar da aikin karɓar su tare da haɗin gwiwar hukumar NEMA da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Nijeriya da kuma Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), tare da tallafin wasu hukumomi da dama.

Bayan isowar tasu, sai jami’an kula da shige da fice na ƙasar sun gudanar da rajista da ɗaukar bayanansu don tabbatar da sahihancin bayanai da kuma sauƙaƙa shirin sake saka su cikin al’umma.

Rukunin mutanen da suka koma sun ƙunshi maza manya 88 da mata manya 32, sai yara maza 14 da kuma yara mata 16.

Bayan an kammala rajista, an kai su masauki a ranar 24 ga Oktoban, 2025 domin ci gaba da tantance su.

Dangane da kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa dawowar ‘yan ƙasa ta kasance lafiya, cikin mutunci da tausayi, an samar musu da tallafin jin kai kai tsaye.

Jami’an sun bayyana cewa haɗin kai tsakanin NEMA, IOM, NCFRMI, da sauran hukumomi ya tabbatar da cewa aikin karɓar ya gudana cikin tsari da inganci, tare da mai da hankali kan mutunci da walwalar waɗanda suka dawo.