Nijeriya ta samu bukatar neman takardar zama dan kasa daga mutum 170 daga ‘yan kasashe da dama.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wajen wani taro na Kwamitin da ke ba da shawara kan ba da shaidar zama ‘yan Nijeriya da aka gudanar a Abuja.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na ma’aikatar ya fitar bayan taron, ta jaddada cewa samun shaidar zama dan Nijeriya alfarma ce da ba za a iya samunta ba sai dole idan mutun yana da mutunci da halayya ta gari.
Sanarwar ta kara da cewa dole ne kwamitin ya tantance wadanda suka shigar da neman shaidar zama ‘yan Nijeriyar da kyau.
Ministan Harkokin Cikin Gidan ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta amince da duk wani abu da wasu ke yi na samun shaidar zama ‘yan Nijeriya ta haramtattun hanyoyi ba, yana mai cewa dole ne a dinga mutunta sahihan hanyoyin samun shaidar a koyaushe.
Da yake sake jaddada shirin Shugaba Bola Tinubu na Sabunta Fata, Tunji-Ojo ya lura cewa aikin kwamitin yana goyon bayan muradun gwamnati na kare mutuncin ƙasa da tsaro, da wadata.










