NIJERIYA
2 minti karatu
Jami'ar ABU Zariya ta musanta zargin gudanar da aikin samar da makamin nukiliya
Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na jami’ar ya ce bidiyon da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI an yi shi ne domin yaudara da ruɗar da jama’a game da shirin Nijeriya na amfani da makamashin nukiliya domin zaman lafiya.
Jami'ar ABU Zariya ta musanta zargin gudanar da aikin samar da makamin nukiliya
Jami'ar ta ce zuwa shekarar 1987, kayan aikin nukiliya kawai da jami’ar ke da shi shi ne 14 MeV Neutron Generator, wanda ya fara aiki a 1988. / Others
10 awanni baya

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ƙaryata wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar tana da hannu wajen samar da makamin nukiliya ga Nijeriya.

Malam Auwalu Umar, Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na jami’ar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Daraktan ya bayyana wannan bidiyon da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI a matsayin abin yaudara da ke neman ruɗar da jama’a game da shirin Nijeriya na amfani da makamashin nukiliya domin zaman lafiya.

Ya ce bidiyon ya yi ikirari na ƙarya cewa wasu masana kimiyya na Nijeriya a shekarun 1980 sun ɓoye sun yi aikin haɓaka sinadarin uranium a Kaduna zuwa ƙarfin amfani da shi domin haɗa makami, tare da cewa masu bincike daga ABU sun samo kayan inganta Uranium daga ƙungiyar AQ Khan a ƙasar Pakistan.

Umar ya ƙara da cewa wannan bayani ba shi da tushe.

Ya bayyana cewa mafi yawan masana kimiyyar ABU da ke Cibiyar Bincike da Horarwa kan Makamashin Nukiliya (CERT) a lokacin shekarun 1980 suna kan karatu a ƙasashen waje, don haka ba za su iya shiga aikin haɓaka uranium ba.

Daraktan ya ce ABU ba ta da wata alaƙa da ƙungiyar AQ Khan kuma ba ta taɓa karɓar wasu kayan aiki da za ta iya amfani da su wajen samar da na’urar haɓaka uranium domin yin makamin nukiliya ba.

Ya ƙara da cewa zuwa shekarar 1987, kayan aikin nukiliya kawai da jami’ar ke da shi shi ne 14 MeV Neutron Generator, wanda ya fara aiki a 1988.

Umar ya jaddada cewa dukkan ayyukan nukiliya na Nijeriya suna gudana ne a fili kuma don manufar zaman lafiya kawai, bisa yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Nuclear Non-Proliferation Treaty (NPT) da kuma Pelindaba Treaty, waɗanda suka haramta kera makaman nukiliya.