NIJERIYA
1 minti karatu
An lalata wani turken rarraba lantarki na Gombe zuwa Damaturu a Nijeriya – TCN
Kamfanin TCN ɗin ya ce tuni injiniyoyinsa suka isa wurin da lamarin ya faru inda suke aikin sauya sabon turken da dawo da wutar.
An lalata wani turken rarraba lantarki na Gombe zuwa Damaturu a Nijeriya – TCN
TCN ɗin ya ce tuni injiniyoyinsa suka isa wurin da lamarin ya faru inda suke aikin sauya sabon turken da dawo da wutar. / NTA
8 awanni baya

Kamfanin dakon wutar lantarki na Nijeriya TCN ya ce an lalata wani turkensa na dakon lantarki da ke kan hanyar Gombe zuwa Damaturu, wanda hakan ya yi sanadin samun katsewar lantarki a Maiduguri da Damaturu da Yobe da wasu sassan yankin.

Sai dai TCN ɗin ya ce a halin yanzu ana samun wutar ne ta tashar samar da lantarki ta ko-ta-kwana ta Maiduguri wanda a halin yanzu take ba tashar samar da lantarki ta Yola wuta.

Kamfanin TCN ɗin ya ce daga yanzu samar da wutar zai koma kan manyan layukan rarraba wuta na 33kV da suka haɗa da Beneshiek da Damasak da Bama da University Campus da birnin Maiduguri da Monguno.

Haka kuma Damaturu za ta samu wuta daga tashar Potiskum a halin yanzu.

TCN ɗin ya ce tuni injiniyoyinsa suka isa wurin da lamarin ya faru inda suke aikin sauya sabon turken da dawo da wutar.

Kamfanin dakon lantarkin ya buƙaci jama’a da su kare kadarorin ƙasa tare da kai ƙarar duk wani abu da suka gani wanda ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.