Da alama gwamnonin Kano da Katsina da Jigawa sun yi farar dabara tun da sanyin safiya domin amfani da damar da gwamnatin kasar ta bayar ta cewa jihohi ko kamfanoni za su iya samar wa kansu wutar lantarki.
A yanzu haka gwamnonin tare da hadin gwiwar kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO sun fara wani yunkuri na hadaka domin samar wa kansu lantarki don amfanin jihohinsu, abin da har ya kai su kasar Maroko domin tattaunawa da kamfanin da za a yi hadin gwiwa da shi.
A karshen makon jiya ne, gwamnonin uku, da suka hada da Abba Kabir Yusuf na Kano, da Dikko Umar Radda na Katsina da Umar Namadi na Jigawa suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar mallakar jari a kamfanin makamashi na Future Energies Africa (FEA), wanda shi kuma zai sanya hannun jari a kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kano KEDCO don bunkasa samar da wutar lantarki.
KEDCO shi ne kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a Jigawa da Kano da Katsina.
Bayanai sun ce gwamnatocin uku za su kafa wani asusu da za su saka naira biliyan hamsin a kamfanin na (FEA).
Shirin zai bunkasa samar da wutar lantarki ne a jihohin ta fuskoki da dama, musamman samar da wutar daga hasken rana.
Da wannan yunkuri, jihohin uku sun kama hanyar shiga jerin jihohin Nijeriya da suke so ko ma tuni suka rungumi harkokin samar da wuta a karan-kansu, da kuma amfani da ita ga jama’arsu, bayan sahhalewar gwamnatin tarayya.
A watan Yunin 2023 ne Shugaban kasar Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar Dokar Lantarki da ta sakar wa jihohi mara cewa za su iya samar wa kansu wutar lantarki su kuma rarraba ta ga al'ummarsu.
Tun daga lokacin jihohi da dama sun fara cin moriyar tsarin ta hanyar aiki da shi a matakai daban-daban, to amma dai wannan ne karon farko da wasu jihohin suka hada kansu domin samar da wutar da kuma raba ta tsakaninsu, matakin da Jaridar Daily Trust ta ce zai iya zama abin koyi ga jihohin kasar ta fuskar inganta harkokin lantarki.
A halin da ake yanzu, KEDCO na daga kamfanonin rarraba lantarki da suka fi samun mafi karancin wuta daga kamfanin raba wutar lantarki na kasa TCN, sannan ga tsadar wutar idan aka kwatanta da wasu kamfanin rarraba wutar lantarkin da ke kudancin kasar.
Hakan ta sa masana’antu da dama daga Kano suka durkushe, wasu suka yi kaura zuwa Legas da Ogun, inda ake samun wuta sosai kuma mafi araha, kamar yadda Alhaji Sani Husaini Sale, mamba na kwamitin koli na kungiyar masu masana’antu ta kasa kuma tsohon shugaban kungiyar reshen Kano da Jigawa ya bayyana wa TRT.
Don haka ne ma ya ce matakin gwamnonin ya faranta musu rai, kuma in dai har an yi nasara, masana’antun jihohin uku za su bunkasa, kuma har ma wasu daga wasu sassan kasar da ma kasar waje za su yi rige-rigen bude masana’antu a jihohin.
Sai dai Alhaji Sani ya bai wa gwamnonin shawarar cewa su fi mayar da hankali kan samar da wutar daga iskar gas, musamman idan an kammala aikin bututun gas na AKK, wanda ya ce shi ne abin da aka fi amfani da shi a kudu, kuma shi ya sa wutar ta fi sauki a can.
Shi ma Alhaji Ali Safiyanu Madugu, wani jigo kuma fitacce a harkar masana’antu a arewacin Nijeriya ya jinjina wa gwamnonin, sannan ya yi kira a gare su da su ci gaba da irin wannan hadaka kan batutuwan tattalin arzikin jihohinsu.
Ku ya kuke kallon wannan mataki na gwamnonin Katsina da Jigawa Kano? Ku bayyana mana a comment section.