NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Amurka ta soke bizar Wole Soyinka ta haramta masa shiga kasar
“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka, Don haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,” in ji Soyinka.
Gwamnatin Amurka ta soke bizar Wole Soyinka ta haramta masa shiga kasar
Wole Soyinka / Reuters
6 awanni baya

Kasar Amurka karkashin Shugabanta Donald Trump ta soke bizar mashahurin marubucin nan, wanda ya taba lashe kyautar Nobel ta adabi, dan Nijeriya, Farfesa Wole Soyinka.

Marubucin ya sanar da hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talata.

Ya ce ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har ya sa aka kwace masa bizar.

“Ya zama dole ne na kira wannan taron saboda mutanen Amurka da ke tsammanin zuwana wasu taruka da cewa kar su bata lokacinsu.

“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka, Don haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,” ya ce.

A cewar Soyinka, Ofishin Jakadancin Amurka ne suka sanar da shi batun kwace bizar a wata wasika da suka aike masa.

"Har yanzu ina duba tarihina na baya... Ba ni da wani tarihin aikata laifuka na baya ko ma babban laifi ko rashin da'a da zai sa in cancanci a soke min biza."

"Na fara waiwayen baya—shin na taɓa yin wani rashin adalci ga Amurka? Shin ina da wani mugun tarihi? An yanke min hukunci? Shin na saba wa doka a ko'ina?"

Sukar Trump

Wole Soyinka ya kasance mai yawan sukar Trump.

A lokacin da Trump ke neman zama shugaban Amurka a karon farko, Soyinka ya ce zai lalata katin shaidar zamansa ɗan ƙasa na Amurka idan aka ayyana Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Bayan nasarar Trump, malamin ya cika wannan alƙawarin kuma ya nisanta kansa daga Amurka.

Duk da haka, bayan an yanke wa Trump hukunci a lokacin da yake shirin komawa Fadar White House, Soyinka ya nuna cewa zai iya sake neman izinin zama na dindindin a Amurka.

Idan za a tuna, an yanke wa Trump hukunci kan tuhume-tuhume 34 na karya bayanan kasuwanci.

Da yake mayar da martani ga hukuncin da aka yanke wa Trump a lokacin, Soyinka ya ce yana iya sake duba shawararsa ya sake neman izinin zama na dindindin a Amurka.