Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya wato PENGASSAN ta bayar da umarni a dakatar da jigilar ɗanyen mai da gas ga matatar Dangote domin nuna adawa da korar ɗaruruwan ma’aikata da matatar ta yi a makon nan.
Matakin ƙungiyar ya biyo bayan korar fiye da ma’aikata 800 da ake zargi matatar ta kora a ranar Alhamis, duk da cewa kamfanin na Dangote ya bayyana matakin nasa a matsayin wani ɓangare na “sauya fasalin tsarin ma’aikatar” don magance ayyukan zagon-ƙasa.
A cikin wata wasiƙa da Sakatare Janar na PENGASSAN, Kwamared Lumumba Okugbawa ya rattaba wa hannu, wadda aka aike ga shugabannin rassan ƙungiyar a manyan kamfanonin mai—ciki har da TotalEnergies, Chevron, Shell Nigeria Gas, Oando, Renaissance, da Seplat Producing Nigeria Unlimited, ƙungiyar ta bayar da umarnin a dakatar da duk wani aikin lodin ɗanyen mai da gas da nufin jigilarsa zuwa matatar Dangote.
“Shugaban NGIC, ya tabbatar an dakatar da isar da gas zuwa matatar nan take daga yanzu,” in ji wasiƙar.
PENGASSAN ta bayyana korar ma’aikatan a matsayin abin da bai dace ba kuma ba za a yarda da shi ba, musamman ma bayan ɗaukar matakin ba tare da shawara da ƙungiyar ba.
Duk da cewa matatar ta ce korar ma’aikatan ya zama dole ne don magance “ayyukan zagon-ƙasa” da kuma tabbatar da tsaron wurin aiki, shugabannin ƙwadagon sun ƙi amincewa da wannan hujja inda suka nemi a dawo da dukkan ma’aikatan da abin ya shafa nan take tare da kiran a gudanar da tattaunawa cikin gaskiya.