| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe sojojin Nijeriya tara a mummunan harin kwanton-ɓauna a Jihar Borno
A baya bayan nan ‘yanta’addar ISWAP da Boko Haram sun tsananta kai hare-hare a yankin arewa maso-gabashin Nijeriya.
An kashe sojojin Nijeriya tara a mummunan harin kwanton-ɓauna a Jihar Borno
Yankin arewa maso-gabashin Nijeriya na fama da rikice-rikicen 'yan bindiga. / Reuters
6 Janairu 2026

Rahotanni daga majiyoyin tsaro biyu sun ce aƙalla sojojin Najeriya tara ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata lokacin da ayarin motocinsu ya taka nakiya da sannan aka buɗe musu wuta a Jihar Borno da ke arewa maso-gabashin ƙasar.

An kai harin ne a ranar Lahadi kusa da kauyen Bindundul, kimanin kilomita 20 daga Kareto, wani yanki da mayaƙan ƙungiyar IS reshen yammacin Afirka (ISWAP) masu alaƙa da Daesh ke cin karensu babu babbaka inda galibi suna kafa shingayen binciken ababen hawa, a cewar wata majiyar soji daga rundunar sojoji ta Damasak.

"'Yanta'addan sun dasa nakiyar da sojojinmu suka taka. Abin takaici, kimanin sojoji tara ne suka mutu nan-take, yayin da wasu biyar suka ji munanan raunuka," in ji Abba Kaka Tuja, wani mamba na rundunar haɗin gwiwa ta fararen-hula da ke da aikin ceto.

Ya ƙara da cewa an lalata wata mota mai sulke lokacin da nakiyar ta fashe, sannan aka fuskanci harbin bindiga daga 'yanta’addan.

Tsananta kai hare-hare

Sojojin suna kan hanyarsu daga Maiduguri zuwa Damasak, hedkwatar ƙaramar hukumar Mobbar, lokacin da harin ya afku da misalin ƙarfe 16:00 GMT, in ji Tuja.

Jami'an soji ba su bayar da amsa nan-take ga buƙatar yin tsokaci ba.

Yankin arewa maso-gabashin Nijeriya, inda mayaƙan ISWAP da Boko Haram suka tsananta kai hare-hare a watannin baya bayan nan, suna nufar ayarin sojoji da fararen-hula, shi ne yankin da ya fi fuskantar rikici a ƙasar.

Sauran yankunan ƙasar ma na cikin tashin hankali.

Amurka ta kai hari kan 'yanbindiga a arewa maso yamma a ƙarshen watan da ya gabata.