TURKIYYA
1 minti karatu
Turkiya na goyon bayan duk wani ƙoƙari na kawo ƙarshen kisan kiyashi a Gaza: Erdogan
Erdogan ya ce yana fatan yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin ɓangarorin biyu za ta haifar da zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali da samar da tsaro a Gaza da sauran yankunan Falasɗinawa.
Turkiya na goyon bayan duk wani ƙoƙari na kawo ƙarshen kisan kiyashi a Gaza: Erdogan
Erdogan ya buƙaci Isra'ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza / AA
7 awanni baya

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana goyon bayan ƙasarsa ga duk wani shiri da zai kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza.

“Muna goyon bayan duk wani tsari da zai kawo ƙarshen kashe-kashe da kisan kiyashin da ake yi a Gaza tsawon shekaru biyu,” in ji shi a wani jawabi da ya yi a birnin Rize na yankin Bahar Aswad.

Ya ƙara da cewa, “Turkiyya ta nuna matsaya mai adalci da gaskiya a cikin tsarin da ya kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.”

Erdogan ya bayyana fatan Turkiyya kan cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas za ta haifar da zaman lafiya mai dorewa, kwanciyar hankali, da tsaro a Gaza da sauran yankunan Falasɗinu.

“’Yan’uwanmu Falasɗinawa, musamman Hamas, sun nuna cewa suna shirye don zaman lafiya,” in ji shi.

Shugaban ya yi kira ga Isra'ila da ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta sanya hannu a kanta, tare da kawo ƙarshen manufofinta na tashin hankali da ke barazana ga yankin da tsaron al'ummarsa.

“Yanzu, dole ne gwamnatin Isra'ila ta bi sharuɗɗan wannan yarjejeniya,” in ji Erdogan.