TURKIYYA
4 minti karatu
Ayarin Sumud yunƙuri ne mai kyau na hana Isra'ila kisan kiyashi a Gaza: Hakan Fidan
Fidan ya bayyana cewa bayan tsare waɗanda ke cikin jiragen ruwan Flotilla, Ankara ta ƙaddamar da wani shiri na diflomasiyya don tabbatar da sakin su.
Ayarin Sumud yunƙuri ne mai kyau na hana Isra'ila kisan kiyashi a Gaza: Hakan Fidan
Fidan ya bayyana furucin Shugaban Amurka Donald Trump na adawa da mamayar Isra’ila a yankin Yammacin Kogin Jordan a matsayin wani juyin al’amura. / AA
5 awanni baya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yaba wa mutanen da ke cikin jiragen ruwa na Global Sumud Flotilla, inda ya kiran ƙoƙarinsu da “abin alfahari” don wayar da kan duniya game da rikicin da ake ci gaba da yi a Gaza da kuma dakatar da Isra’ila ci gaba da kisan ƙare-dangi a yankin Falasɗinawa da ta yi wa ƙawanya.

Fidan ya jaddada cewa wannan shirin na taimako na Flotilla, wanda ya shafi ƙasashe da dama da kuma jiragen ruwa da yawa, an tsara shi da kyau don ya kasance cikin lumana kuma a guji tada hankali a yankin.

“Babban burinmu shi ne wannan ya yi nasara ba tare da tashin hankali ba kuma mu tabbatar da dawowar ‘yan kasarmu lafiya,” in ji shi a wata hira da aka yi da shi a TRT Haber a ranar Asabar.

Fidan ya bayyana cewa Turkiyya ta yi aiki tare da ƙawance na ƙasashe, ciki har da Sifaniya da wasu ƙasashen Latin Amurka da Asiya-Pacific, don matsin lamba ga Isra’ila ta fuskar ƙasa da ƙasa.

Ya ce wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ministocin harkokin wajen ƙasashe 17 suka fitar a ranar 16 ga Satumba wani ɓangare ne na wannan dabarar diflomasiyya.

A cikin sanarwar, Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya, Bangladesh, Brazil, Colombia, Indonesia, Ireland, Libya, Malaysia, Maldives, Mexico, Pakistan, Qatar, Oman, Slovenia, Afirka ta Kudu, Sifaniya, da Thailand sun nuna damuwarsu game da tsaron jiragen ruwa na Global Sumud Flotilla.

“Ba kawai wani shiri na farar hula bane; ƙasashe sun tsaya a bayansa, cikin iyakokin dokar ƙasa da ƙasa,” in ji Fidan, yana yaba wa Sifaniya saboda rawar da ta taka da kuma haɗin kai.

Bayan tsare waɗanda ke cikin jiragen ruwan, Ankara ta ƙaddamar da wani shiri na diflomasiyya don tabbatar da sakin su.

“Shugabanmu [Erdogan] ya bayar da umarni kai tsaye. Ta hanyar haɗin kai tsakanin hukumar leken asiri, ma’aikatar harkokin wajenmu, da sauran abokan hulda, mun dawo da ‘yan kasarmu,” in ji Fidan, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin sakin waɗanda ke tsare.

Lokacin juyin al’amura

Fidan ya bayyana furucin Shugaban Amurka Donald Trump na adawa da mamayar Isra’ila a yankin Yammacin Kogin Jordan a matsayin wani juyin al’amura.

“Sanarwar Shugaban Amurka Trump cewa ba zai yarda da mamayar yankin Yammacin Kogin Jordan ba, hakika, wani juyin al’amura ne na tarihi,” in ji shi.

Sai dai Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya nuna damuwa cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na iya kawo cikas ga shirin Trump na tsagaita wuta a Gaza.

“Akwai yiwuwar Netanyahu zai lalata shirin Trump, kuma ina ganin akwai wannan niyya,” in ji shi.

Yayin da yake haskaka ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyyar Turkiyya wajen kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila a Gaza, yana nuni da shirin Hamas na sakin dukkan waɗanda suka kama daga Isra’ila, Fidan ya ce, “Jiya, Shugaba Trump ya kira Shugabanmu Erdogan. Awanni shida zuwa bakwai bayan tattaunawarsu, Hamas ta bayar da amsa mai kyau da wata sanarwa.”

“Dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu (Erdogan da Trump) ta kuma kasance mai amfani wajen kokarin samun tsagaita wuta a Gaza; wannan yana nuna cewa hadin kansu ba kawai yana taimakawa wajen warware matsalolin da ke tsakaninsu ba, har ma yana ba da gudummawa ga zaman lafiya a yankin,” ya kara da cewa.

Fidan ya kammala da tabbatar da kudurin Turkiyya na tallafa wa shirye-shiryen farar hula masu zaman lafiya da kuma motsa duniya don ɗaukar mataki na adalci a Gaza.

Game da Syria

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya kuma yi kira da a ɗauki matakai masu ƙarfi don kare haɗin kan kasar Syria, yana mai cewa dukkan abubuwan da ke barazana ga dunƙulewar ƙasar dole ne a kawar da su.

“Abubuwan da ke kawo barazana ga dunƙulewar Syria da rarrabuwar ƙasar dole ne a kawar da su.”

Ya jaddada cewa dole ne YPG ta fayyace niyyarta kuma ta cim ma yarjejeniya da Damascus.

“YPG dole ne ta bayyana niyyarta a fili kuma ta cim ma yarjejeniya da Damascus.”

Yayin da yake magana kan rikice-rikicen da ke kudancin Syria, Fidan ya kuma jaddada bukatar samun mafita mai kyau ga matsalar Druze, wadda za ta mutunta haɗin kan ƙasar kuma ta kasance abin karba ga dukkan bangarori.

“Matsalar Druze a kudancin dole ne a warware ta cikin kyakkyawan yanayi, daga hangen nesa da za a karba daga dukkan bangarori, ba tare da kawo barazana ga hadin kan kasar ba,” kamar yadda ya kara da cewa.