Matar shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi jimamin cika shekaru biyu na yaƙin Isra'ila a Gaza, inda ta yi tir da abin da ta bayyana a matsayin yunƙurin Isra'ila na shafe al'ummar Falasɗinu daga doron duniya.
"Ƙasar da ta rasa mutuncinta tana ƙoƙarin ruguza al'ummar Falasɗinu daga doron duniya,’’ a cewar wani saƙo da Erdogan ta wallafa a shafinta na NSosyal na Turkiyya.
"Duk da cewa zaluncin azzaluman na ƙaruwa, ƙarfin muryoyin haɗin-kai na tasirin kan kisan ƙare-dangi," in ji ta.
Erdogan ta ce, a cikin shekaru biyu da suka wuce, Gaza ta zama maƙabarta inda aka kashe mutane fiye da 67,000 da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da yara fiye da 20,000.
Ta jadadda cewa, a hare-hare da Isra’ila ke kaiwa, ‘‘babu wani mutunci, ko doka ko jinƙai, ko kuma ɗa’a da ba a keta shi ba."
Emine Erdogan ta ƙara da cewa, masu aikin sa-kai suna yin gangami don Gaza daga kowane lungu da saƙo na duniya, ta sama, ta ƙasa, da kuma ta ruwa, tana nuni ne kan ayarin jiragen ruwa na Sumud na baya bayan nan da suka yi ƙoƙarin zuwa yankin da aka yi wa ƙawanya, ta kuma yi kira ga “duk wani mutum mai tausayi da ya shiga wannan fafutuka da kuma haɗa kai a matsayin ɗaya daga cikin Falasɗinawa har sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa.”
"Ina tunawa da 'yan’uwanmu Falasɗinawa da suka yi shahada a hare-haren Isra'ila, kuma ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya sassauta wa al'ummar Falasɗinu tare da ƙara masu haƙuri da juriya da tsayin daka. #EndlessGenocideGaza," in ji ta.
Saƙon ya kuma haɗa da wani bidiyo da ke ɗauke da jawaban Emine Erdogan na baya kan Gaza da kuma hotuna da ke nuna ɓarnar da aka yi a yankin.