TURKIYYA
3 minti karatu
Erdogan a UNGA: 'Ba yaƙi kawai ake yi a Gaza ba, kisan ƙare dangi ake yi'
Shugaban Turkiyya ya nemi duniya ta dauki mataki a kan mugunta da cin zalin da Isra'ila ta shafe kusan shekara biyu tanayi a Gaza, yana cewa ana kashe yaro ɗaya a duk cikin awa ɗaya har tsawon wata 23.
Erdogan a UNGA: 'Ba yaƙi kawai ake yi a Gaza ba, kisan ƙare dangi ake yi'
Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce bala'in ɗan'adam da ke Gaza babu misalinsa a tarihin zamani. / AA
7 awanni baya

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi jawabi mai zafi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York, inda ya zargi Isra'ila da aikata kisan kare dangi a Gaza, tare da kira ga al'ummar duniya su dauki mataki cikin gaggawa don kawo ƙarshen zubar da jini.

“A gaban kowa da kowa, ana ci gaba da kisan kare dangi a Gaza fiye da kwanaki 700,” in ji Erdogan a ranar Talata.

“A cikin watanni 23 da suka gabata, Isra'ila tana kashe yaro guda a kowace awa. Wannan ba wai alƙaluma ba ne kawai; ko wanne ɗaya rai ne, mutum ne mara laifi.”

Erdogan ya bayyana cewa bala'in jinƙai da ke faruwa a Gaza ba shi da misali a tarihin zamani, inda ya ce yara ƙanana masu shekaru biyu ko uku suna rasa gabobin jikinsu ba tare da samun maganin kashe raɗaɗi ba.

“Wannan shi ne mafi ƙasƙancin abin da aka taɓa yi a tarihin ɗan’adam,” ya faɗa wa shugabannin duniya. “Ba yaƙi ake yi a Gaza ba, tun da babu ɓangarori biyu. Wannan mamaya ce, kisan ƙare dangi ne kuma manufofin kisan gilla ne.”

‘Ina magana a madadin al’ummar Falasɗinu’

Shugaban ƙasar Turkiyya ya gode wa ƙasashen da suka amince da kafa ƙasar Falasɗinu kuma ya yi kira ga sauran ƙasashe su “dauki mataki ba tare da ɓata lokaci ba.”

Ya nuna rashin jin daɗinsa cewa Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas bai halarci taron a New York ba, yana mai jaddada cewa Turkiyya tana magana “a madadin al’ummar Falasɗinu, waɗanda aka hana su damar yin magana.”

Erdogan ya yi kira da a samu tsagaita wuta nan take a Gaza, a ba da damar kai agajin jinƙai ba tare da wani cikas ba, tare da tabbatar da adalci ga abin da ya kira “ƙungiyar kisan ƙare dangi ta Isra’ila.”

Ya zargi Isra’ila da faɗaɗa hare-harenta fiye da Gaza da yankin Yammacin Kogin Jordan zuwa Siriya, Iran, Yemen, Lebanon da Qatar, yana mai cewa hakan na barazana ga zaman lafiya a yankin gaba ɗaya.

“Da ra’ayin ƙasar da aka yi alkawari, gwamnatin Isra’ila tana lalata zaman lafiya a yankin da kuma nasarorin da ɗan’adam ya samu tare da manufofinta na faɗaɗa,” in ji Erdogan, yana mai cewa Firaminista Benjamin Netanyahu “ba shi da niyyar zaman lafiya ko sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.”

‘Ku tsaya tare da Falasɗinawa masu shan wahala’

Shugaban ƙasar Turkiyya ya yi kira ga shugabannin duniya su tsaya “ƙyam tare da Falasɗinawa masu shan wahala a yau a madadin ɗan’adam,” yana mai cewa hare-haren Isra’ila sun kawar da mafi ƙarancin haƙƙin ɗan’adam, ciki har da haƙƙin mata da yara, ‘yancin faɗar albarkacin baki, daidaito, da kuma adalci.

“Za a iya samun zaman lafiya a duniya a inda yara ke mutuwa saboda yunwa da rashin magani?” in ji Erdogan. “Ɗan’adam bai taɓa ganin irin wannan zalunci a ƙarni na ƙarshe ba.”