Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sun yi alƙawarin ƙara yauƙaƙa dangantaka ta ɓangaren tsaro da kasuwanci yayin tattaunawarsu a Fadar White House a ranar Alhamis.
Trump ya ce shi da Erdogan za su tattauna kan yadda Turkiyya za ta sayi jiragen yaƙi da Amurka ta ƙera, ciki har da jiragen F-16 da F-35, tare da haɗin gwiwar tattalin arziki.
“Muna shirin yin yarjejeniyar kasuwanci mai kyau ga ƙasashen biyu,” in ji Trump ga manema labarai, inda ya ƙara da cewa akwai yiwuwar “nan take” a cire takunkumin da aka sanya wa Ankara saboda sayen makaman roka na Rasha.
A zaune kusa da Trump a ofishin shugaban ƙasa na Oval Office, Erdogan ya ce tattaunawar za ta haɗa da fannoni da dama, ciki har da sayar da kayan tsaro.
“Muna ɗaukar matakai mabambanta a dangantakar Turkiyya da Amurka,” in ji shi. “Ina da yaƙinin cewa tare da haɗa hannu tare, za mu shawo kan waɗannan matsaloli a yankin.”
Trump ya yaba wa takwaransa kan cewa “mutum ne da ake girmamawa ƙwarai,” yana mai cewa ana girmama Erdogan “ƙwarai a kasarsa, da kuma a duk fadin Turai, da ma duniya baki ɗaya.”
Taron ya gudana ne a cikin yanayin da aka daɗe ana samun saɓani tsakanin abokan NATO kan batun sayen makamai, rikice-rikicen yankin, da takunkumin kudi. Amma shugabannin biyu sun nuna yanayin sulhu, inda suka jaddada haɗin kai fiye da sabani.