TURKIYYA
2 minti karatu
Hukumar leƙen asirin Turkiyya ta kama wani mai bincike da ake zargi da yi wa Mossad aiki
Jami’an tsaro sun ce wanda ake zargin ya yi wa Mossad aiki kuma yana magana da Faysal Rasheed, wani da yake aiki a cibiyar intanet ta Isra’ila.
Hukumar leƙen asirin Turkiyya ta kama wani mai bincike da ake zargi da yi wa Mossad aiki
Rahotannin sun ce an biya Cicek dala $4,000 ta hanyar kirifto ranar 1 ga watan Agusta domin yin aikin. / Photo: Others
3 Oktoba 2025

Turkiyya ta bayyana ranar Jumma’a cewa ta kama wani mai bincike mai zaman kansa da ake zargi da yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila Mossad aiki. Wanda ake zargin an kama shi ne a wani samame na haɗin gwiwa da ya haɗa da masu gabatar da ƙara da ‘yan sanda a Istanbul, in ji jami’an tsaro.

Hukumar leƙen asirin ƙasa ta Turkiyya ko MIT, ta ce mutumin da ake zargin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Serkan Cicek, an kama shi ne yayin wani samame mai taken Metron Activity.

Jami’an tsaro sun ce mutumin ya kasance yana yi wa Mossad aiki kuma suna tuntuɓar juna da Faysal Rasheed, wani mamba na cibiyar aikin intanet ta Isra’ila.

An yi zargin cewa Cicek ya amsa yin leƙen asiri a Istanbul, bisa buƙatar Rasheed, kan wani mai fafutuka ɗan Falasɗinu wanda yake adawa da manufofin Isra’ila a Gabas Ta Tsakiya.

Hukumar leƙen asirin Turkiyya ta ce, Cicek — wanda ainihin sunansa  shi ne Muhammet Fatih Keles — ya sauya sunansa ne bayan basussuka sun masa yawa kuma ya bar kasuwancinsa domin kafa kamfani mai zaman kansa, mai suna Pandora Detective Agency, a shekarar 2020.

An ce ya yi aiki ga Musa Kus, wanda aka yi wa ɗaurin shekara 19 a gidan yari bisa laifin yi wa Isra’ila leƙen asiri, da kuma lauya Tugrulhan Dip, inda aka sami su biyu da laifin sayar da bayanan mutane daga rumbun bayan gwamnati domin cin riba.