Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana cewa, 'yan kasar Turkiyya 36 da sojojin Isra’ila suka kama a cikin jiragen ruwan Global Sumud Flotilla a cikin tekun duniya za su koma gida, Turkiyya da yammacin yau ta jirgi na musamman.
“Adadin karshe bai tabbatar ba tukuna. Muna ci gaba da ƙoƙarin kammala dukkan matakan da suka dace don ganin sauran 'yan kasarmu sun dawo gida cikin gaggawa,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a shafinsa na X a ranar Asabar.
Ya ƙara da cewa jirgin da aka shirya zai kuma dauki wasu 'yan kasashen waje.
An kama masu fafutuka fiye da 470
Kungiyar Freedom Flotilla Coalition, wata gamayyar ƙungiyoyin al’umma ta ƙasa da ƙasa, ta sha yunƙurin ratsa ƙawanyar da aka yi wa Gaza tun daga shekarar 2010 don jawo hankalin duniya kan matsalar jin kai a yankin.
Sojojin ruwa na Isra’ila sun kai hari tare da ƙwace jiragen ruwan Global Sumud Flotilla a ranar Alhamis, inda suka kama masu fafutuka fiye da 470 daga ƙasashe fiye da 50.
Jiragen sun yi ƙoƙarin kai tallafin jin ƙai zuwa Gaza da kuma ƙalubalantar takunkumin da Isra’ila ta ƙaƙaba wa yankin.
Isra’ila ta ci gaba da yi wa Gaza ƙawanya, inda mutane kusan miliyan 2.4 ke zaune, tsawon kusan shekaru 18. Tun daga watan Oktoban 2023, hare-haren bama-baman Isra’ila sun kashe kusan Falasɗinawa 66,300 a yankin, yawancinsu mata da yara, tare da sanya yankin cikin mawuyacin hali, yayin da takunkumin ya jefa Gaza cikin yunwa.