Shirin kawar da shara na Zero Waste a Turkiyya wanda matar shugaban ƙasar Emine Erdogan ke jagoranta, ya cika shekaru takwas a bana, wanda hakan ke nuna ƙudurin ƙasar wajen ɗorewar kula da muhalli.
An ƙaddamar da wannan shiri ne a ranar 27 ga Satumbar 2017, ƙarƙashin jagorancin Emine Erdogan, kuma ya bunƙasa zuwa wani shiri na duniya wanda ke ƙarfafa amfani da albarkatu yadda ya kamata, rage ɓarnar, da wayar da kan jama’a.
A ƙarƙashin taken "Shekara ta 8 don Mutane Biliyan 8," shirin yana ci gaba da bunƙasa ta hanyar yaɗa saƙonni a kafafen sada zumunta. Ma’aikatar Muhalli, Tsarin Birane da Sauyin Yanayi ce ke kula da wannan shiri, wanda ya cim ma nasarori masu yawa a fannin tanadin makamashi, rage hayakin iskar gas, sarrafa shara, da kuma tanadin tattalin arziki.
A cikin shekaru takwas, an samar da tsarin na kawar da shara a gine-gine 205,000, inda aka daga darajar sake amfani da shara (recycling) daga kashi 13 cikin 100 a shekarar 2017 zuwa kashi 36.08 cikin 100 a shekarar 2024, tare da burin kaiwa kashi 60 cikin 100 nan da shekarar 2035.
An sake amfani da kimanin tan miliyan 74.5 na kayan da za a iya sake amfani da su, ciki har da takarda, robobi, gilashi, ƙarafa, da kayan abinci, wanda ya samar da Lira biliyan 256 ga tattalin arzikin ƙasar.
Haka kuma, shirin ya hana sare itatuwa miliyan 552.7, ya ta adana lita tiriliyan 1.71 ta ruwa, lita biliyan 54.6 na man fetur, da kuma kilowatt-hour biliyan 227.3 na makamashi, tare da rage fitar da tan miliyan 150 na hayakin iskar carbon dioxide.
Sannan takwaransa na teku wato "Zero Waste Blue" wanda ya shafi teku, an ƙaddamar da shi a ranar 10 ga Yuni, 2019, kuma ya cire kimanin tan 585,000 na shara daga bakin tekun Turkiyya. Wannan shiri ya haɗa da tsarin dawo da kwalabe, wanda ke tattara kwalaben abin sha 50,000 a kullum, tare da shirin faɗaɗa shi a duk faɗin ƙasar.
Kokarin Turkiyya ya samu karɓuwa a duniya
A watan Disamba na shekarar 2022, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana ranar 30 ga Maris a matsayin "Ranar Zero Waste ta Duniya."
Emine Erdogan ta zama uwargidan shugaba ta farko daga Turkiyya da ta yi jawabi a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya a wani zama na musamman kan Zero Waste, inda aka kafa Kwamitin Shawara na Manyan Hukumomi kan Zero Waste ƙarƙashin jagorancinta.
A yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 78, Turkiyya ta shirya taron "Towards a Global Zero Waste Movement" a Turkevi, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya zama na farko da ya sanya hannu kan "Global Zero Waste Goodwill Declaration," wanda Emine Erdogan ta jagoranta.
Tun lokacin ƙaddamar da shirin, dandalin yanar gizo ya jawo hankalin masu sa kai fiye da 15,000 daga ƙasashe 114. Fiye da matan shugabanni 50 na duniya, wakilan manyan ƙungiyoyi na duniya, da ministocin harkokin waje sun amince da wannan sanarwa, wanda ke nuna yadda shirin ke samun karɓuwa a duniya.
A kwanan nan, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80, Emine Erdogan ta gana da Zita Oligui Nguema, matar Shugaban Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema, wadda ta nuna sha’awar amfani da tsarin Zero Waste na Turkiyya da haɗin gwiwa kan shirye-shirye masu ɗorewa.
Erdogan ta tabbatar da cewa Gidauniyar Zero Waste za ta iya bayar da horo da tallafi na fasaha don taimaka wa Gabon wajen aiwatar da wannan shiri. Haka kuma, shirin ya samu karɓuwa a sauran tarukan duniya, ciki har da amincewar ƙasashen G20 da "Global Zero Waste Goodwill Declaration" a lokacin shugabancin Indiya na 2023.
Jagorancin Emine Erdogan ya sa shirin ya samu lambobin yabo na duniya da dama, ciki har da lambar yabo ta FAO "Zero Hunger, Zero Waste" (2018), lambar yabo ta UNDP kan Manufofin Ci gaba Mai Dorewa (2021), lambar yabo ta UN-Habitat Waste Wise Cities Global Champion (2021), lambar yabo ta Majalisar Dokokin Bahar Rum (2022), da lambar yabo ta Bankin Duniya kan Jagorancin Sauyin Yanayi da Ci gaba (2022).