| hausa
TURKIYYA
5 minti karatu
Matar Shugaban Turkiyya ta yi gargaɗi kan 'baƙin zamani' da ruwa ya zama makamin kisan kiyashi
Matar Shugabar Turkiyya Emine Erdogan ta yi gargaɗi kan wani zamani wanda ake ciki kan yadda ake amfani da ruwa a matsayin makami domin aikata kisan kiyashi a Gaza.
Matar Shugaban Turkiyya ta yi gargaɗi kan 'baƙin zamani' da ruwa ya zama makamin kisan kiyashi
Emine Erdogan ta bayyana kare muhalli a matsayin wajibi
25 Satumba 2025

Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan, kuma shugabar babban kwamitin shawara na Majalisar Ɗinkin Duniya kan shirinta na kawar da shara (Zero Waste), ta bayyana cewa duniya na fuskantar wani “baƙin zamani” inda ake amfani da ruwa a matsayin “makamin kisan ƙare-fangi”, inda take nuni da Gaza a matsayin mafi munin misali.

Ta bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da take magana a wajen buɗe baje-kolin “Zero Waste Blue—Drop by Drop” a birnin New York, inda ta ce ƙoƙarin da Turkiyya ke yi a kan muhalli ana yin sa ne don amfanin dukkan bil’adama.

“Muna ɗaukar kowane mataki ba kawai don kanmu ba, amma don dukkan ‘yan’uwanmu da muke zaune a duniya ɗaya da su. Kowace nasara tana kawo mana farin ciki mai ban mamaki na taimaka wa jin daɗin bil’adama,” in ji ta.

Emine Erdogan ta yi gargaɗin cewa Gaza yanzu tana da “ruwa mafi tsada a duniya, domin ana biyan farashin kofi ɗaya na ruwa da rayuwar bil’adama.”

“Abin takaici, muna cikin wani lokaci mai duhu inda ruwa zai iya zama kayan kisan kare-dangi. Tun daga ranar 7 ga Oktobar 2023, Isra’ila ta rinƙa kai hari kan wuraren samar ruwa a Gaza.

“Kimanin kashi 85 cikin 100 na bututun ruwa, matatun ruwa, rijiyoyi, da sauran tsarin samar da ruwa sun zama marasa amfani,” in ji matar Erdogan, tana ƙara cewa ana tilasta wa Falasɗinawa yin tafiya mai nisa kowace rana don samun ruwa don buƙatun yau da kullum.

“Wani lokaci ana kashe su ta hanyar kai musu hare-hare da makamai masu linzami yayin da suke cikin layin ruwa kafin su iya kawo ruwa ga iyalansu.

“Hotunan ƙananan yara suna gwagwarmayar ɗaukar jarkokin ruwa masu nauyi fiye da jikinsu suna zama abin kunya ga lamirin bil’adama,” in ji ta.

“Saboda ƙishirwa, ana tilasta wa mutane shan ruwa wanda bai dace a sha ba. Ina ganin babu wani jan layi ta ɓangaren kima da shari’a ko bil’adama da ya rage ba a tsallaka ba.”.”

Matsalolin roba da ke barazana ga ruwan duniya

Baje-kolin yana da nufin gabatar da ƙoƙarin Turkiyya wajen kare tekuna da tafkuna a matakin duniya da inganta nasarorin muhalli da suke a bayyane, da ƙarfafa haɗin kai na ƙasa da ƙasa don ƙarfafa diflomasiyyar muhalli.

A wannan yanayin, ta jaddada barazanar gaggawa ta gurɓacewar muhalli, tana cewa, “Wa zai yi tunanin cewa bil’adama, wanda ya gina al’ummomi, ya cim ma nasarorin kimiyya, kuma ya samar da ayyukan fasaha masu ban mamaki, wata rana zai samar da wata nahiya cike da shara zai kawar da shuɗin launin sararin samaniyarmu zuwa abin da ba a gane ba?

“Abin takaici, Tekun Pacific kaɗai yana ɗauke da shara wadda ta taso a samar ruwa wanda ta kai murabba’in kilomita miliyan 1.6, wanda ya ƙunshi kwalaben filastik, jakunkuna, bututun sigari, da kuma ragar kamun kifi.

“Wannan yanki ya ninka girman Turkiyya sau biyu, yana nuna girman ƙalubalen da muke fuskanta,” kamar yadda ta ƙara da cewa.

Ta jaddada gurɓacewar da kayayyakin roba na filastik a duniya ke jawowa, inda take cewa “Ana samar da tan miliyan 57 na sharar filastik a duk shekara a duniya, inda kimanin tan miliyan 23 ke gurɓata tafkuna, koguna, da tekuna — daidai da manyan motoci 2,000 na shara da ake zubarwa cikin ruwa kowace rana.

“Ana ƙiyasta fiye da tan miliyan 14 na ƙananan robobi suna cikin tekuna, suna shiga cikin abincinmu har ma suna isa teburinmu.”

Zero Waste ya muhimmin batu a duniya

Emine Erdogan ta bayyana kare muhalli a matsayin wajibi na ɗabi’a wanda ya samo asali daga al’adu, tana cewa, “Abin haɗin kai na kowace tsohuwar al’umma shi ne dangantaka mai girmamawa da yanayi.

“Don fuskantar ƙalubalen sauyin yanayi na duniya a yau, dole ne mu farfaɗo da wannan fahimtar.”

Yayin da take jaddada sadaukarwar tarihi ta ƙasar wajen magance ƙalubalen bil’adama, Erdogan ta tuna da ƙaddamar da tafiyar Zero Waste a shekarar 2017 ƙarƙashin taken “Duniyarmu, Gidanmu Na Bai ɗaya.”

Ta bayyana cewa Zero Waste yanzu ya zama muhimmin batu na duniya, tana ambaton amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya ta shekarar 2022 kan ƙudurin Zero Waste da kuma Sanarwar Kyakkyawar Niyya ta Zero Waste ta Duniya da Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya goyi bayan.

Tun daga shekarar 2019, shirin Zero Waste Blue ya cire tan 285,000 na shara daga teku, wanda ya yi daidai da manyan motoci 22,000 na shara, daga bakin tekun Turkiyya da tekuna. Kamfen na 2023 kan Ingantaccen Amfani da Ruwa ya ƙara jaddada sadaukarwar Turkiyya wajen tabbatar da samun ruwan sha mai lafiya a duniya inda fiye da mutane biliyan 2 ba su da shi.

Ta kammala da kira ga duniya mai adalci inda ruwa da abinci ba su kasance makamai ba, da kuma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

Emine Erdogan ta gayyaci mahalarta su sanya hannu kan Sanarwar Kyakkyawan Niyya ta Zero Waste ta Duniya a matsayin alƙawari na haɗin kai kan alhakin muhalli. Bayan jawabin nata, Ministan Sauyin Yanayi da Makamashi na Australiya, Chris Bowen, ya sanya hannu kan sanarwar a hukumance.

Rumbun Labarai
Turkiyya ta yi umarnin kama Firaministan Isra'ila Netanyahu da wasu mutane kan kisan kiyashi a Gaza
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista
Turkiyya na da rawar da za ta taka a tsaron Turai, ta shirya domin aikin Gaza: Ministan Tsaro
Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin TRCN kan ƙudurin samar da ƙasashe biyu