Turkiyya ta dage haraje-harajen da ta sanya a kayayyakin Amurka da ake shiga da su kasarta kamar motoci da ’ya’yan itatuwa gabanin wata ganawa tsakanin Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan da Shugaban Amurka Donald Trump nan gaba a wannan mako.
Galibin kudin haraje-haraje da Turkiyya ta rage wasu ta sanya su ne a shekarar 2018 lokacin da Trump ya nunka kudin haraji a kan kayan kayayyakin Turkiyya, kamar ma’adanin steel da aluminium.
Daga nan ne sai Turkiyya ta mayar da martani, inda ta nunka haraje-haraje kan kayayyakin Amurka misali motoci da barasa da taba sigari.
Turkiyya ta bayyana martanin da yi da wani “mataki” kan tattalin arzikin Turkiyya.
Matakin Turkiyya na baya-bayan nan na rage haraje-haraje kan kayayyakin Amurka wata alama ce ta kyautatuwar alaka tsakanin Turkiyya da Amurka.
Trump ya ce yana saran kammala yarjejeniyar kasuwanci da ta soji yayin wata ziyara da Shugaba Erdogan yake yi a Amurka.
Gwamnatin Trump tana amfani da karawa kasashe haraje-haraje a matsayin wani makami na yaki da abokan gabanta a fannin tattalin arziki kamar Rasha hatta ma Indiya da Kanada.
A watan jiya ne Amurka ta sanar cewa za ta sanya harajin kaso 15 cikin 100 na kayayykin da ake shiga da su Amurka daga Turkiyya.
A nata martanin Turkiyya ba ta sauya harajin da take sanya wa kayan Amurka.
Ministan Cinikayya na Turkiyya ya ce yanzu Amurka tana kallon Turkiyya a matsayin “kawa kuma abokiyar kasuwanci.”
“Wannan wata babbar dama ce da Turkiyya ta samu idan aka kwatanta da sauran kasashen yankin Asiya da Latin Amurka,” a wata sanarwa da ma’aikata cinikayya ta kasar ta bayyana.