'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
AFIRKA
5 minti karatu
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher"Fyaɗen taron dangi ake yi. A bainar jama’a ake yi wamata fyaɗe, a gaban kowa kuma babu wanda ya iya dakatar da hakan," in ji Amira ta bayyana daga wani matsuguni na wucin gadi a Tawila, kimanin kilomita 70 yamma da Al Fasher.
A makon da ya gabata, MDD ta ce an yi wa akalla mata 25 fyade a lokacin da 'yan tawayen RSF suka shiga wani sansani.
6 awanni baya

Wata uwa ‘yar Sudan mai suna Amira ta bayyana yadda a kowace rana take wayar gari cikin fargaba da kaduwa, saboda tuna masifar da ta shaida ta yadda ake yi wa mata fyade a yayin da suke tserewa daga birnin Al Fasher da ke yammacin kasar bayan da ‘yan tawaye suka kwace iko da birnin.

Bayan kawanyar da aka shafe wata 18 ana yi wa birnin, wadda ta janyo yunwa da hare-hare, Al Fasher - sansanin sojoji na ƙarshe a yankin yammacin Darfur - a ranar 26 ga Oktoba ya fada hannun rundunar ‘yan tawaye ta (RSF), waɗanda ke yaƙi da sojoji tun daga watan Afrilun 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama, an ci zarafin mata, an kai hare-haren kan ma'aikatan agaji, da sace-sace da kuma satar mutane a birnin da aka katse hanyoyin sadarwa a cikinsa.

"Fyaɗen taron dangi ake yi. A bainar jama’a ake yi wamata fyaɗe, a gaban kowa kuma babu wanda ya iya dakatar da hakan," in ji Amira ta bayyana daga wani matsuguni na wucin gadi a Tawila, kimanin kilomita 70 yamma da Al Fasher.

Amira uwar 'ya'ya huɗu ta yi magana a lokacin wani taron intanet da ƙungiyar kamfen ta Avaaz ta shirya tare da wasu da suka tsira daga tashin hankalin da aka yi kwanan nan.

Avaaz bai bayyana sunaye da fuskokin waɗanda suka shiga cikin hirar ta intanet ba saboda ba su kariya.

Kungiyar (MSF) ta ce fiye da mata 300 da suka tsira daga cin zarafin suna samun kulawa daga ƙungiyoyinsu a Tawila bayan wani hari da RSF ta kai a sansanin Zamzam da ke kusa, wanda ya raba mutum fiye da 380,000 da muhallinsu a bazarar da ta gabata.

"Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International a watan Afrilu ta yi gargadin cewa, RSF ta aikata cin zarafin mata a garuruwa da kauyuka a Sudan domin wulakanta su, da tabbatar da iko da kuma tilasta wa iyalai da al'ummomi korarsu daga gidajensu."

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi bayani game da cin zarafin mata da sojoji da RSF suka yi - musamman a babban birnin Khartoum da Darfur - kuma ta ce ya kamata a yi tur tare da "hukunta irin wadannan laifuka na tsawon shekara 20, musamman na RSF".

Bala’in cin zarafi

A Korma, wani ƙauye mai nisan kilomita 40 arewa maso yammacin Al Fasher, Amira ta ce an tsare ta na tsawon kwana biyu saboda ba za ta iya biyan mayaƙan RSF kuɗin wucewa lafiya ba.

Ta ce waɗanda ba za su iya biya ba, an hana su abinci, ruwa da ikon fita, kuma an kai hare-hare da yawa da daddare.

"Idan kika sake kika yi barci to za su zo su yi miki fyaɗe," in ji ta.

"Na ga mutanen da ba za su iya biyan kuɗi da idona ba, kuma mayakan sun ɗauki 'ya'yansu mata maimakon haka.

"Sun ce, 'Tun da ba za ka iya biya ba, za mu ɗauki 'yan matan.' Idan kana da 'ya'ya mata ƙanana, za su ɗauke su nan take."

Ministan jin dadin jama'a na Sudan, Sulimah Ishaq, ya shaida wa AFP cewa an kashe mata 300 a ranar da Al Fasher ta fadi zuwa hannun RSF, "wasu bayan an ci zarafinsu ta hanyar jima'i".

Kungiyar Agajin Gaggawa da 'Yan Gudun Hijira a Darfur, wata kungiya mai zaman kanta ta agaji, ta rubuta kararraki 150 na cin zarafin mata tun bayan faduwar Al Fasher har zuwa ranar 1 ga Nuwamba.

"Wasu abubuwan sun faru a Al Fasher wasu kuma a lokacin gudunsu zuwa Tawila," in ji Adam Rojal, mai magana da yawun kungiyar, ga AFP.

Fyade da bakin bindiga

A makon da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da rahotanni masu tayar da hankali cewa an yi wa akalla mata 25 fyade a lokacin da sojojin RSF suka shiga wata mafaka da mutanen da suka rasa matsuguni ke zama a kusa da Jami'ar Al Fasher da ke yammacin birnin.

"Shaidu sun tabbatar da cewa jami'an RSF sun zaɓi mata da 'yan mata kuma suka yi musu fyade ta hanyar rutsa su da bindiga," in ji Seif Magango, mai magana da yawun ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, a Geneva.

Mohamed, wani wanda ya tsira daga harin da ya shiga taron intanet na Avaaz daga Tawila, inda ya bayyana yadda aka nemi mata da 'yan mata a kowane mataki aka kuma wulakanta su a Garni, wani gari tsakanin Al Fasher da Tawila.

"Idan ba su sami komai a kanka ba, sai su yi maka duka. Sun bincike 'yan matan, har ma sun yaga kunzugunsu wato pad na tare al’ada," in ji shi.

A Garni, kafin su isa Korma, Amira ta ce shugabannin RSF za su "gaisa da mutane", amma da zarar sun tafi, mayakan da suka tsaya a baya suka fara azabtar da su.

"Suna fara sanya ka a cikin jerin sunayen: 'Kai soja ne.' 'Kana da alaƙa da sojoji,'" in ji ta.

Ta kuma bayyana yadda ta ga mayakan RSF suna yanka maza da wukake. "Ɗana mai shekaru 12 ma ya ga hakan, kuma yanzu yana cikin mummunan yanayi na rudu," in ji ta.

"Mun farka muna kyarma saboda tsoro, hotunan yadda ake yanka mutane suna ta gilmawa ta idanuwanmu."

Fiye da mutum 65,000 ne suka tsere daga Al Fasher tun bayan faduwarta, ciki har da sama da mutum 5,000 waɗanda yanzu haka ke neman mafaka a Tawila, wadda ta riga ta ɗauki nauyin 'yan gudun hijira sama da 650,000, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A Tawila, ɗaruruwan mutane sun taru a cikin tantuna na wucin gadi a wani babban yanki na hamada, suna tattara duk abin da za su iya don shirya abinci ga iyalansu, kamar yadda bidiyon AFP ya nuna.

Rojal na Kungiyar Haɗa Kan Mutanen da Aka Kora da 'Yan Gudun Hijira a Darfur ya yi gargaɗin cewa lamarin "yana buƙatar shiga tsakani ba tare da bata lokaci ba.”