Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar a ranar Alhamis cewa tana maraba da cim ma tsagaita wuta a Gaza, tare da fatan hakan zai kawo karshen kisan kiyashin da ake ci gaba da yi tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Yayin da ake sa ran aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma gaba ɗaya, sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, "duba da tsagaita wutar da aka yi, ya zama wajibi a kai agajin jinƙai zuwa Gaza-inda bala'in jinƙai ya yi tsanani, kuma za a ƙaddamar da yunƙurin sake gina Gaza ba tare da ɓata lokaci ba. Turkiyya za ta ci gaba da bayar da taimakon jinƙai mai yawan gaske a yankin Gaza."
Sanarwar da ke nuni da cewa, za a iya samun dauwamammen zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar ɗaukar matakan adalci a batun Isra'ila da Falasɗinu, ta bayyana fatan ma'aikatar "cewa nasarar da aka cim ma kan tsagaita wuta za ta bayar da gudummawa wajen tabbatar da samar da ƙasashe biyu nan gaba."
Sanarwar ta ce, "Muna yaba wa ƙoƙarin Qatar, da Masar, da Amurka wajen shiga tsakani a samar da yarjejeniyar tsagaita wuta. Turkiyya ta jaddada ƙudirinta na bayar da gudunmawa sosai tare da ba da goyon bayanta a duk matakan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar," in ji sanarwar.
Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya ya yi maraba da yarjejeniyar
Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz ma ya yi maraba da cim ma tsagaita wutar, a wata sanarwa ta daban a ya fitar a shafin sanadwar yanar gizo na Turkiyya NSocial.
"Duk da cewa an daɗe ana yaƙi, muna maraba da tsagaita wuta a Gaza, muna miƙa godiyarmu ga duk wanda ya ba da gudummawarsa ga wannan sakamako, musamman ga shugabanmu Recep Tayyip Erdogan," in ji shi, inda ya ƙara da cewa: "Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Falasɗinu, kamar yadda ta saba yi.
"Tare da hana ci gaba da zubar da jinin Falasdinawan da ba su ji ba ba su gani ba, da kai agajin jin ƙai ba tare da cikas ba, da kuma fara yunƙurin sake gina Gaza za ta shiga wani sabon shafi."
Yilmaz ya ce, Turkiyya za ta sa ido sosai kan yadda ake aiki da yarjejeniyar tare da ci gaba da ba da goyon baya.
Ya ƙara da cewa, "A ƙarshe, kawo ƙarshen mamayar da kafa ƙasar Falasdinu bisa iyakokin shekarar 1967, tare da Gabashin Ƙudus a matsayin babban birninta, zai tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kowa da kowa."