TURKIYYA
4 minti karatu
Turkiyya ta yi imanin cewa iyali ne hanyar samun adalci da zaman lafiya —Matar Shugaban Turkiyya
Emine Erdogan ta yi kira da a samar da tsari na musamman a MDD domin jagorantar matakan ƙarfafa fasalin iyali.
Turkiyya ta yi imanin cewa iyali ne hanyar samun adalci da zaman lafiya —Matar Shugaban Turkiyya
Iyali shi ne mai ɗaukar ɗabi’u da kuma wuri mafi tsaro ga yaranmu da kuma makomar bil Adama, kamar yadda ta bayyana. / AA
13 awanni baya

Turkiyya ta yi imanin cewa hanyar zaman lafiya da adalci da kuma wadata ga kowa ita ce hanyar iyali, kamar yadda matar shugaban ƙasar Emine Erdogan ta bayyana.

Da take magana a wani shiri mai taken "[Mun] fi dacewa tare: Haɗin kan duniya da ke da asali a iyali," a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 80 a birnin New York, Emine Erdogan ta ce iyali ba kawai muhimmin ɓangare ne na al’umma ba, shi ne muhimmin mataki na ci-gaba mai ɗorewa ga zamantakewa da tattalin arziki da al’ada.

Erdogan ta yi kira da a samar da tsari na musamman a cikin MDD domin jagorantar matakan ƙarfafa fasalin iyali. “Ya kamata a kafa wani tsari kocokan a cikin MDD domin jagorantar aiki kan ƙarfafa iyali,” a cewarta.

Erdogan ta yi gargaɗin cewa iyali a wannan zamanin na “fuskantar ƙalubale” da ya haɗa da sauyin yanayi da yaƙe-yaƙe da ɗabi’u marasa kyawu da aƙidu marasa nuna bambancin jinsi.

Ta bayyana cewa yanayin haihuwa na raguwa sosai a duniya tun shekarun 1950, inda sakin aure ya ƙaru kuma ana samun ƙaruwar iyaye maza ko mata da ke tafiyar da harkokin gida su kaɗai bayan rabuwar aure.

“Manufofi da suka mayar da hankali kan iyali a yanzu ba zaɓi ba ne, abubuwa ne da suka wajaba,” kamar yadda ta jaddada, tana mai ƙarawa da cewa iyalai masu ƙarfi suna da alaƙa kai-tsaye da zaman lafiya da kuma ingancin al’ummomi.

“Kimanin ƙananan yara miliyan 50 sun rasa muhalli a halin yanzu”

Ta kuma bayyana hatsarin da harkar intanet ke yi inda yara ke shafe fiye da sa’o’i shida a ko wace rana a gaban talbijin, waya ko komfuta kuma suke kallon miyagun aƙidun cin zarafi.

“Yanayin ayyuka na zamani ba sa tallafa wa mata a matsayinsu na iyaye da kuma cikin rayuwa ta iyali,” in ji ta.

Da take ishara ga binciken da ke nuna yadda yawan laifuka ke ƙaruwa sosai a birane da ke da yawan mace-macen aure, Erdogan ta ce fasalin iyali cibiya ce ta farko ta warware matsalolin zamantakewa.

“A iyalai masu nagarta, yara suna girma a matsayin masu tausayi da girmamawa da kuma zaman lafiya,” kamar yadda ta bayyana.

Da take magana game da tashin hankali na duniya, ta jaddada cewa sau da yawa iyali ne ke kasancewa abu na farko da yaƙe-yaƙe da tashe-tashen hankula ke lalatawa.

“A yau bala’i na marayu mafi girma a duniya a tarihi na wannan zamanin yana aukuwa a Gaza. An tagayyara ɗaruruwan iyalai a gaban idanunmu, an bar dubban yara ba tare da iyayensu ko makoma ba,” a cewarta, inda ta yi ishara ga Sudan da Yemen da Myanmar da kuma Ukraine a matsayin misalai. Kusan yara miliyan 50 ne aka raba da gidajensu, a cewarta.

“Goyon bayan iyali "

Fasalin iyal shi ne ginshiƙi da ya fi samar da tsaro ga yaranmu kuma makomar bil’adama, kamar yadda ta bayyana, tana mai ƙarawa da cewa a lokacin tashin hankali da yaƙe-yaƙe da bala’o’i, "gaskiyar da ke mana jagoranci ita ce haɗin kai na farawa ne daga iyali."

“Iya yadda za mu iya kare iyali, iya yadda za mu iya gina duniya mai adalci da zaman lafiya da wadata," kamar yadda Erdogan ta bayyana, tana mai kira ga MDD ta ɗauki ƙarfafa iyali a matsayin wata manufa mai zaman kanta.

Ta kuma bayyana ƙarfin gwiwarta cewa ko wane ra’ayi da shawara da aka gabatar a wannan batu zai ƙarfafa matakan duniya domin kare iyali.

Zaman dai ma’aikatar iyali ta Turkiyya ta karɓi baƙuncinta kuma ministoci daga ƙasashen Qatar da Hungary da Saliyo da Somaliya da Nijeriya da Sabiya da kuma wakilai daga Rasha da Amurka sun halarce shi.