Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
DUNIYA
5 minti karatu
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamaiBijirewa antibiotic na kara ta’azzara a Afirka, yana mayar da cututtuka suke zama barazana, a yayinda tsarin kula da lafiya da marasa lafiyar ke fafutuka da tsadar zuwa asibiti, karancin kayan gwaji da bijirewar antibiotic d ajiki ke yi.
Bijire wa antibiotic da jiki ke yi ya zama babban hatsari ga kula da lafiya a Afirka. / WHO
6 awanni baya

Adebayo, wani malami mai shekaru 32 a Legas, ya yi tunanin ya kamu da wani ciwo na yanayi a lokacin da zazzabi da tari suka kama shi.

Ya kamata magungunan antibiotic su magance cutar tasa. Amma ba su warkar da ita ba. Cikin 'yan kwanaki sai yanayinsa ya kara ta'azzara.

Gwaje-gwaje sun nuna cewa yana da wata mummunar cuta da kwayoyin cutar Klebsiella pneumoniae ke janyowa.

Abin tsoro shi ne kusan babu wani abu a cikin kantin sayar da magunguna na asibiti da zai iya shawo kan cutar.

"Na ji tsoro sosai, ba kawai daga rashin lafiyar ba, har ma da rashin taimakon waɗanda ke yi mini magani," Adebayo ya shaida wa TRT Afrika.

"Magungunan da ake da su ba su da amfani a gare ni. Likitoci suna ta faman yawo, kuma na makale a cikin wani tarko da ban fahimta ba."

A ƙarshe an ceci rayuwarsa ta hanyar maganin antibiotic mai tsada.Magani ne wanda ya rage ga mutane ‘yan kadan a cikin nahiyar.

Daduwar bijirewa

Abinda ya samu Adebayo ya nuna wani rikici da ke faruwa a faɗin Afirka da kuma wasu wuraren. Wani sabon rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa mutum ɗaya cikin shida na kamuwa da ƙwayoyin cuta a duniya da a yanzu suke bijire wa antibiotic, inda girman barazanar ke ƙaruwa da kashi 5-15% a kowace shekara.

A Yankin Afirka na WHO, adadin ya fi haka. Mutum ɗaya cikin kowane biyar da aka tabbatar da kamuwa da cuta a dakin gwaje-gwaje yana nuna jikinsa na bijire wa magungunan antibiotic.

Ma'aikatan kiwon lafiya a faɗin ƙasashe suna fama da sakamakon amfani da maganin antibiotic ta ci barkatai wanda ke haifar da bijirewar a kowace rana.

A Cape Town, Afirka ta Kudu, ma'aikaciyar jinya Anathi Bhengu ta shaida yadda rikicin ke ƙaru wa tsawon shekaru.

"Muna fuskantar wannan yanayi kowace rana. Cututtukan da ya kamata a shawo kansu da sauƙi ta hanyar amfani da magunguna suna zama barazana ga rayuwa," in ji Bhengu ga TRT Afrika. "Bayan haka, ana gogayya da lokaci don nemo maganin da ke aiki."

Asibitin Bhengu ya aiwatar da shirye-shiryen kula da maganin antibiotic masu tsauri don hana amfani da maganin ta ci barkatai.

"Yanzu muna yin gwaji da sauri, muna mai da hankali kan magani da ke aiki, kuma muna ilmantar da kowane majiyyaci cewa maganin antibiotic ba ya maganin mura ko tari. Hanyar shawo kan wannan ƙalubalen ita ce a yi taka tsantsan da canza yadda muke amfani da magunguna masu ceton rai."

WHO ta kiyasta cewa bijirewar antibiotic ya fi yawa a yankin kudu maso gabashin Asiya da yankin Gabashin Bahar Rum, kodayake Afirka ma tana fuskantar matsalar.

Ƙasashen da ke da tsarin kiwon lafiya da aka yi masa yawa kamar Najeriya, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Kenya suna da rauni.

Hakan na zuwa ne saboda asibitoci da yawa ba su da ikon gano ƙwayoyin cuta masu bijire wa da sauri kuma ana fuskantar tsadar kula da lafiya a kasashen.

Kamu wa da cututtuka

Bijiewar antibiotic na zama babban hatsari idan marasa lafiya ba su dauki matakin amfani da magungunan da aka zaɓa na farko ga ƙwayoyin cuta irin su E. coli da Klebsiella pneumoniae ba, waɗanda dukkan su na haifar da kamu wa da cututtukan jini masu hatsari.

A Afirka, bijirewar magungunan da aka zaɓa na farko ga waɗannan ƙwayoyin cuta ya haura kashi 70%.

To, ta yaya ƙasashen Afirka ke ƙara daukar matakai kan waɗannan barazanar?

Sanarwar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 kan bijirewar ƙwayoyin cuta ya bayyana ɗaukar hanyar "Lafiya Ɗaya". Wannan yana nufin yin aiki mai kyau a fannin lafiyar ɗan adam, lafiyar dabbobi, da kuma kare muhalli.

Ƙasashe mambobi sun riga sun ƙarfafa tsarin ayyukan dakin gwaje-gwajensu da inganta sa ido ta hanyar Tsarin Kula da Lafiya na Duniya na WHO (GLASS).

Shiga cikin tsarin ya ninka sau huɗu tun daga 2016. Manufar ita ce dukkan ƙasashe su ba da rahoton bayanai masu inganci nan da 2030, wanda zai tabbatar da cewa ka’idojin yin magani sun dogara ne akan yanayin bijire wa na gida.

"Bijirewar ƙwayoyin cuta na wuce ci gaban da aka samu a fannin likitancin zamani, wanda ke barazana ga lafiyar iyalai a duk duniya," in ji babban daraktan WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, yayin da yake jaddada bukatar amfani da maganin antibiotic mai inganci, samun magunguna da gwaje-gwaje daidai gwargwado, da kuma kirkire-kirkire don samar da sabbin magunguna.

Ga waɗanda suka tsira kamar Adebayo, tsoron abin da zai iya faru wa a gaba idan kamu wa da cuta ya ya ki tafiya.

"Ina ɗaya ne daga cikin waɗanda suka yi sa'a, amma ina kuma tunanin waɗanda ba su yi ba," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afrika.

"Dole ne mu tabbatar da cewa bijirewar maganin antibiotic ba ya zama annoba ga al’ummu masu zuwa. Wani dan karamin ciwo ko rashin lafiya ta yau da kullun na iya zama hukuncin kisa."