Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi gargaɗi a ranar Jumma’a cewa komawa ga “yanayi na kisan kiyashi” a Gaza zai haifar da “babban martani,” yayin da yake maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
An cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a safiyar Alhamis a Sharm el-Sheikh na Masar, bisa shirin matakai 20 da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.
Mataki na farko na shirin ya hada da tsagaita wuta nan take, sakin wadanda aka yi garkuwa da su da fursunoni, janyewar Isra’ila zuwa layin da aka amince da shi a Gaza, da kuma isar da tallafin jin kai zuwa Gaza tare da goyon bayan kasa da kasa don sake gina yankin.
Yayin da yake jawabi a wani biki na kaddamar da sabbin gine-gine da ayyuka a lardin Rize na Tekun Bahar Maliya, Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya ta yi — kuma za ta ci gaba da yin — duk mai yiwuwa don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali a Gaza “da wuri-wuri.”
‘A daina zubar da jini’
Da yake magana kan yarjejeniyar tsagaita wuta, Erdogan ya jaddada cewa “abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne tabbatar da cewa an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata,” yana mai cewa Ankara za ta taka rawa mai muhimmanci a wannan tsari.
“Yankinmu, musamman Gaza, ya sha wahala sosai daga zubar da jini, kisan gilla, da hawaye,” in ji shi. “Dole ne a ba zaman lafiya dama, kuma a guji duk wani abu da zai kawo cikas.”
Erdogan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “babban mataki” zuwa ga zaman lafiya mai ɗorewa duk da ƙalubalen da ke gaba. “An buɗe ƙofar zaman lafiya ta dindindin a Gaza,” in ji shi. “Muna cewa — a daina zubar da jini.”
Amurka ta tabbatar cewa sojojin Isra’ila sun kammala janyewa zuwa layin rawaya a mataki na farko. Bisa yarjejeniyar, Hamas za ta saki mutane 20 da aka yi garkuwa da su tare da mayar da gawarwaki 28, yayin da Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 250 da ke da hukuncin daurin rai da rai da kuma mutane 1,700 da aka kama tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.