TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Erdogan ya jaddada goyon bayan Turkiyya na kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.
Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Shugaban Turkiyya Erdogan ya jinjina wa Falasɗinawa bisa jajircewarsu da mutunta kawunansu / AA
9 Oktoba 2025

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana gamsuwarsa game da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta Falasɗinawa bayan tattaunawar da aka yi a birnin Sharm el-Sheikh na ƙasar Masar, wada Turkiyya ta taka rawa a cikinta.

A sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, Erdogan ya gode wa shugaban Amurka Donald Trump bisa nuna dattako na siyasa wajen sanyawa Isra’ila ta saka hannu kan yarjejeniyar, kana ya miƙa godiya ga ƙasashen Qatar da Masar bisa muhimmiyar rawar da suka taka wajen cim ma yarjejeniyar.

Shugaban ƙasar Turkiyya ya ce Turkiyya za ta bibiyi aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar kuma za ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya.

Ya jaddada matsayin Ankara wajen samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta bisa iyakokin da aka shata a shekarar 1967 da kuma Gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birninta.

Da yake nuna goyon bayansa ga Falasɗinawa waɗanda suka kasance cikin uƙuba da tafka asara a shekaru biyu da suka wuce, Erdogan ya jinjina musu game da jajircewarsu da kuma martabarsu duk da mawuyacin halin da suke ciki.

Ana sa ran saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza da Trump ke jagoranta da misalin ƙarfe 0900 GMT a Masar, kamar yadda wata majiya da ke da sanayya kan lamarin ta shaida wa Reuters ranar Alhamis.

Kazalika ana sa rai yarjejeniyar za ta soma aiki da Gaza da zarar an sanya mata hannu, a cewar majiyar.