Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ƙara ƙaimi a yaƙin nema wa Nijeriya kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin ganawarsa da Sakatare Janar na MDD, António Guterres a hedkwatar majalisar da ke New York, Shettima ya jaddada cewa Nijeriya ta cancanci samun goyon baya mai ƙarfi daga ƙasashen duniya, yana mai nuni da irin rawar da kasar ke takawa wajen samar da zaman lafiya, da dimokuradiyya, da zaman lafiyar yankin.
Tattaunawar ta kuma shafi sauyin yanayi, da ci gaba mai ɗorewa, da haɗin gwiwar Nijeriya da shirin raya ƙasa na Majalisar Dinkin Duniya.
Ministoci a tawagar Mataimakin Shugaban Ƙasar sun ce Guterres ya yaba da ci gaban da Nijeriya ta samu a fannin fasahar ƙere-ƙere, musamman yadda aka ƙaddamar da tsarin fara amfani da yare da yaruka da yawa da wata gwamnati ta taɓa kafawa a Afirka.
Mista Guterres ya tabbatar wa Nijeriya cewa za a ci gaba da ba ta tallafi.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Ƙasar Kashim Shettima ya kuma gana da Mataimakin Firaministan Birtaniya David Lammy, inda bangarorin biyu suka amince da zurfafa hadin gwiwa a fannonin ciniki, tsaro, da kuma ƙaura.
Har ila yau, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bi sahun shugabannin kasashen duniya a taron majalisar jagoranci na duniya, inda ya tabbatar da cewa hada kan dijital da karfafa matasa sun kasance a mahimmai a gun Shugaba Bola Tinubu.