Morocco ta doke Faransa da ci 5-4 a bugun fenareti ranar Laraba, inda ta samu gurbi a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta ‘Yan Ƙasa da Shekara 20.
Wannan ne karon farko da ƙasar de ke arewacin Afirka ta samu kai wa wannan mataki.
Mai tsaron ragar Faransa, Lisandru Olmeta ya zura ƙwallo a ragarsa a minti na 32 wanda ya bai wa Morocco fifiko, kafin ɗan wasan tsakiyar Faransa, Lucas Michel ya farke a minti na 59.
An kai minti 90 ana da ci 1-1, amma ana dab da cikar ƙarin lokaci sai kocin Morocco, Mohamed Ouahbi, ya saka sabon gola, Abdelhakim El Mesbahi don ya tsare musu ragar yayin bugun fenareti.
An bai wa El Mesbahi hotunan 'yan wasan Faransa a jikin robar ruwansa, tare da ƙananan zane-zanen da ke nuna inda za su iya doka ƙwallonsu ta fenariti.
Kama ƙwallon ƙarshe
Dabarar ta yi aiki domin gola El Mesbahi, wanda bai buga kowanne daga cikin wasannin Morocco a gasar ba, ya tare bugun ƙarshe na Faransa wanda Djylian Nguessan ya buga.
Wannan ne ya kai Morocco zuwa wasan ƙarshe na gasar, inda za ta fafata da Argentina ko Colombia.
Tun da fari, mai tsaron raga na farko na Morocco, Yanis Benchaouch ya ji rauni inda aka maye gurbinsa da Ibrahim Gomis a minti na 64. Shi kuma Gomis ya ba wa El Mesbahi dama a ƙarshen ƙarin lokaci.
Morocco ta yi nasara a rukuninta, bayan doke Sifaniya da Brazil, sannan ta doke Korea ta Kudu da Amurka kafin ta isa wasan kusa da na ƙarshen.
A baya, mafi kyawun sakamakon da Morocco ta samu a gasar shi ne matsayi na huɗu a shekarar 2005.