Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi wa wasu ’yan ƙasar mutum 175 waɗanda kotu ta samu da laifi afuwa ciki har da tsohon ɗan majalisar wakilan ƙasar daga Jihar Kano Farouk Lawan da marigayi Manjo Janar Mamman Vatsa da dan kishin kasa marigayi Herbert Macaulay.
Shugaban ya ɗauki wannan mataki ne bayan samun amincewar Majalisar Magabata ta Ƙasar wadda ta yi wani zama a ranar Alhamis.
Tinubu ya ce ya ɗauki matakin yafe musu ne bayan masu laifin sun nuna nadamarsu da kuma shirinsu na sake komawa cikin al’umma don ci gaba da rayuwa, kamar yadda wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Nijeriyan Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana.
Sauran mutanen da za su ci gajiyar wannan alfarmar ta shugaban ƙasar su ne: Mrs. Anastasia Daniel Nwaobia da Barrister Hussaini Umar da Ayinla Saadu Alanamu da sauransu.
Marigayi Mamman Vatsa soja ne wanda aka samu da laifin cin amanar ƙasa a shekarar 1986, kusan shekara 40 bayan faruwar hakan, sai dai Tinubu ya yafe masa duk da cewa ba ya raye. Kazalika shi ma marigayi Harbert Macaulay wanda ya kasance ɗan kishin ƙasa kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar NCNC. Tinubu ya yi mai afuwa ne kan wani laifi da kotu ta same da aikatawa a shekarar 1913 lokacin Nijeriya tana ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka.
Sannan sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya yafe wa wasu fursunoni 82 da suke tsare a gidan yari, kuma ya rage wa wasu fursunoni 65 wa’adin zaman gidan yari. Kazalika Shugaba Tinubu ya sassauta wa wasu mutum bakwai da aka yankewa hukuncin kisa zuwa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Bugu da ƙari Tinubu ya yafe wa wasu masu fafutuka daga yankin Ogoni ciki har da Ken Saro-Wiwa duk da cewa an riga an zartar musu da hukuncin kisa.
Sanarwar ta ce an tantance mutanen da shugaban ya yi wa afuwa ne bayan an karɓi shawarwari daga wani kwamitin bayar da shawarwari na shugaban ƙasa wanda Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati Prince Lateef Fagbemi (SAN) yake shugabanta.