Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.
“’Yan jarida abokan aikinmu, babu wani abu mai ƙarfi a yanzu da zai hana aiwatar da matsayar kwamitin zartarwa na ASUU ta shiga yajin aikin gargaɗi na makonni biyu bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 14 da aka bayar tun ranar 28 ga Satumban, 2025.
“Saboda haka, duka rassan ASUU an umurce su da su dakatar da ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na daren Litinin, 13 ga Oktoban, 2025.
“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.
Sabuwar taƙaddama tsakanin malaman jami’a da gwamnatin tarayya na zuwa ne duk da ƙoƙarin tattaunawa don kauce wa wani sabon yajin aiki a jami’o’in ƙasar.
A ranar Laraba, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana a Abuja cewa gwamnati ta shiga matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi domin warware matsalolin da suka shafi albashi, kuɗaɗen tallafi, da aiwatar da yarjejeniyar ASUU ta shekarar 2009.