Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda tara sannan sun ceto mutum biyu da ke ɗauke da kuɗin fansa waɗanda za a ba ‘yan ta’adda a yankunan Gajiram da Magumeri na jihar Borno.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Operation Hadin Kai, Laftanal Kanal Uba Sani ya fitar a ranar Asabar ta ce an kashe ‘yan ta’addan ne a lokuta daban daban.
Sani ya bayyana cewa, baya ga makamai da aka ƙwato, da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun samu munanan raunuka kuma sun watse cikin ruɗani.
“A ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci a Arewa Maso Gabas, dakarun Operation HADIN KAI (OPHK) sun kai wani samame da suka yi nasara bayan samun sahihan bayanan sirri kan shawagin ‘yan ta’addan Boko Haram a kusa da Goni Dunari da ke Ƙaramar Hukumar Magumeri ta jihar Borno a ranar 10 ga Oktoban 2025.”
“Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan suna tafe da motoci biyu da mayaƙa 24, suna ƙona gidaje da tsoratar da mazauna yankin. Dakarunmu suka ɗauki mataki cikin gaggawa suka kaddamar da sintirin yaƙi domin tarwatsa barazanar.”
Ya ce yayin da dakarun ke matsowa kusa da wurin, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin gudu zuwa ƙauyen Damjiyakiri.
“’Yan ta’addan da ke cikin motoci sun watse zuwa wani wurin da ba a sani ba, yayin da masu tafiya a ƙafa suka ci gaba da gudu, kuma dakarun suka bi sawunsu na kusan kilomita 92,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayan kusan awanni huɗu na bin sawu cikin dabaru, dakarun suka cim ma ‘yan ta’addan.
“An kaddamar da farmaki kai tsaye, inda dakarun suka yi musu luguden wuta, wanda ya haifar da kashe ‘yan ta’adda biyar, sauran kuwa suka watse cikin ruɗani.
“Wasu sun ji jikkata, saboda an ga jini yana zuba a wurin fafatawar,” in ji shi.
An gano makamai
Sanarwar ta yi ƙarin bayani dangane da irin makaman da aka yi nasarar ƙwatowa waɗanda suka haɗa da Ya lissafa abubuwan da aka kwato da suka haɗa da bindiga ɗaya kirar AK-47 (lambar rajista 06798), ƙundun harsasai biyar (uku babu harsasai, biyu cike), harsasai 31 na 7.62mm, wayar Itel ɗaya, wuka ɗaya.
Ya ƙara da cewa babu asarar rayuka ko kayan aiki daga dakarun OPHK yayin aikin.
A wani aiki na daban, mai magana da yawun ya ce dakarun da ke kan babura sun gwabza da ‘yan Boko Haram a kan hanyar Gajiram–Bolori–Mile 40–Gajiganna, kusa da ƙauyen Zundur na jihar.
Ya bayyana cewa a lokacin harin, an kashe ‘yan ta’adda huɗu, sauran kuma suka tsere cikin daji.
“Dakarun sun kuma ceto Modu Kinnami (mai shekaru 55) da Bukar (mai shekaru 57), duka daga Guzamala, tare da buhun da ke ɗauke da Naira 750,000,” in ji shi.
“Binciken wucin-gadi ya nuna cewa ‘yan Boko Haram sun nemi a biya Naira miliyan 2 da wayoyi biyu sabbi kirar Tecno na latsawa don su saki ɗan uwansu da suka yi garkuwa da shi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dakarun sun ƙwato mota akori-kura mai launin shuɗi (lambar rajista GUB 327 XA), wayoyi biyu sabbi kirar Tecno, jarka ɗaya mai ɗauke da lita 30 na fetir, da jimillar kuɗi har naira miliyan 4 da dubu 355 (₦4,355,000).
Sojoji huɗu sun rasu a Borno
Sojoji huɗu sun mutu, kuma wasu biyar sun ji rauni a ranar Juma’a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari a sansanin soja da ke Ngamdu, kan hanyar Damaturu–Maiduguri a Ƙaramar Hukumar Kaga ta Jihar Borno.
Ya ce, ana ci gaba da gudanar da ayyuka a dukkan ɓangarori domin ci gaba da matsa wa ‘yan ta’addan lamba tare da hana su sakat cikin ‘yanci.