Turkiyya ta ambace shi Rumfar Karfe. Sunan ba na je-ka-na-yi-ka ba ne.
A ranar 6 ga Agustan 2024, Kamfanin tsaro na lataroni na Turkiyya ASLSAN ya kaddamar da Rumfar Karfe (Çelik Kubbe), wani tsarin tsaron sama na gani na fada da Shugaba Racep Tayyip Erdogan ya bayyana a matsayin “wani gagarumin sauyi a karfin Turkiyya na tsaron sama”.
Tsarin, wanda aka samar da shi a cikin gida ba tare da bin tsari irin na kasashen waje ba, an tsara shi ne ta yadda zai bibiyi ya kuma tarwatsa duk wani nau’in farmaki na sojoji daga waje da sauran barazana – daga jirage marasa matuka masu zilliya da ake sarrafa su daga nesa zuwa makamai masu linzami da suke gudu fiye da sauti.
Rumfar Karfe ba wai kawai kayan aikin sojojin sojoji ba ne. Ta wata hanyar, nuna karfin azama ne na kasar da a wani lokacin take hankilon samun tsarin tsaro na Kasashen Yamma. Turkiyya da tuni ta shiga sahun gaba a kasashen duniya da suka fi samar da jiragen yaki marasa matuka, a yanzu tana samar da kayayyakinta na yaki kuma tana aika su fadin nahiyoyi uku.
Tsarin na Rumfar Karfe wanda kamfanin ASELSAN ya samar da hadin gwiwar Roketsan da TÜBİTAK SAGE wata hadaka ce ta abubuwan da ke gano motsi, da cibiyar bayar da umarni da sarrafawa, da kayayyakin yaki masu amfani da laturoni da tsarin makami duka a cikin tsarin mai amfani da AI
Manufarsa ita ce samar da tsarin tsaro mai matakai daban-daban a duka fadin sararin samaniyar Turkiyya, da shirya mayar da martani ga barazana ta sama da ta makamai masu linzami a duk lokacin da aka kawo su.
Ba wai kawai garkuwa ba ce
Tsarin yana gudana akan hanyar sadarwa ta 5G irin ta soja wacce aka ƙera don kiyaye tsaro yayin kutsen yanar gizo ko yaƙin ta na’ura. Cibiyar sadarwarsa mai bibiyar motsi ta haɗa da na’urorin gano abubuwan da suke giftawa daga dangin ALP, masu iya gano barazana daga nisan kilomita 650, wadanda na’urori masu tsarin gani har hanji da na'urorin da suke tallafwa wajen sanya ido a kowane lokaci ba kakkautawa suka taimakawa.
Tsarin bayar da umurni na sarrafawa na ASELSAN HAKİM yana haɗa kowace na’urar da ke bibiyar abubuwan da suke giftawa, da masu ƙaddamar da tsaro da bangarorin na’urorin kayan yaƙi, yana ba da damar auna barazanar kai-tsaye da shirya martani.
Tsarin ya haɗa makaman da aka kera a cikin gida kamar KORKUT, ŞAHİN, HİSAR da SİPER don ƙirƙirar shingen kariya daga barazanar da ta kama daga jirage marasa matuka da ke tafiya kasa-kasa zuwa makamai masu linzami masu cin dogon zango.
Abin da ya bambanta Rumfar ta Karfe shi ne tana amfani da buɗaɗɗun tsare-tsare, abin da ya ba da damar ƙara masa sabbin fasahohi ba tare da sake fasalin baki daya ba. AI dinsa yana nazarin bayanin da ya sunsuno nan-take, inda ya ke jujjuya tsarin daga martani mai ƙarfi zuwa kariyar da aka yi tanadinta gabanin zuwan hari.
Mafi kyawun sashinsa shi ne cewa tsarin tsaro na AI da ya kunshi komai da komai yana koyo kuma yana aiwatar da abin da ya koya a kan lokaci. Shi kuwa tsarin yakin kayan yakinsa na zamani an tsara shi ne ta yadda zai iya sarrafa wuta, don ƙirƙirar abin da wadanda suka samar da shi suka bayyana a matsayin "sarkar kisa" da ke da ikon mayar da martani kan tsararriyar barazana ta daruruwan jirage marasa matuka.
Mai taka rawar gani a harkar tsaro a duniya
Bikin baje-kolin masana'antun tsaro na kasa da kasa da aka gudanar a Istanbul daga ranakun 22 zuwa 27 ga watan Yulin bana ya kasance baje-kolin fasahohi iri-iri da suka hada da tsarin yakin tafi da gidanka na KORAL 200 na ASELSAN, da tsarin yaki da jiragen sama mai karfin gaske na EJDERHA, da tsarin dabarun tattara bayanai na T-LINK.
A watan Agustan da ya gabata ne kamfanin ASELSAN ya cika shekaru 50 da kafuwa, kamfanin ya samar wa Rundunar Sojojin Turkiyya wasu muhimman abubuwa 47 da kudinsu ya kai dalar Amurka miliyan 460.
Jerin kayan aikin sun haɗa da tsarin SİPER, HİSAR, KORKUT, ALP, da kuma tsarin PUHU waɗanda wasu ɓangarori ne na fasahar tsaro da ke ci gaba da haɓaka tsarin tsaro na Turkiyya ta hanyar fasaha.
Shugaba Erdoğan da manyan jami'an gwamnatinsa sun halarci bikin mika kayan a hukumance.
Dabarun 'yancin kai
Zuwan Rumfar Karfe na nuna sauyi a dabarun tsaro na Türkiye zuwa ga wadatar da kai, da nisantar rarrabuwar kawuna zuwa ga hadadden tsarin da ya kunshi komai.
A matsayinsa na dandamali mai basira, wanda ya dace da yanayin da ake bukatarsa wanda kuma yake shirye a aiwatar da shi nan gaba, yana kuma nuna tabbatar da yunƙurin Turkiyya wajen tabbatar dogaro da kai a sama ta hanyar fasahar cikin gida da aka tsara don haɓakawa, da ganowa da magance sabbin barazanar kai-tsaye.
Ayyukan tsaro na ASELSAN sun samu yabo a Amurka, Turai da Gabas ta Tsakiya, ciki har da Qatar, Lebanon, da UAE. Fadada kawancen tsaro da Turkiyya ke yi a fadin nahiyar Afirka ya kara inganta martabar kamfanin da kuma taimakawa wajen kara yawan ayyukansa.
Hadin gwiwar sojojin Afirka
An amince da yarjejeniyoyin tsaro da Kamaru a watan Afrilun 2021, sai kuma yarjejeniyar hadin gwiwa da masana'antun tsaro da Nijeriya a watan Oktoban 2021 yayin ziyarar Shugaba Erdogan a kasar.
Kasashen Afirka da dama - Nijeriya, Nijar da Chadi, a takaice - sun sayi jiragen yaki na UAV, da jirage masu saukar ungulu, jiragen horo, da makami mai linzami daga Turkiyya. Wadannan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje suna taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tsaro da manufofin nahiyar Afirka.
Kwararru sun yi Imani cewa yadda Rumfar karfen ke rikidewa a babban aikin tsaron sama zai karfafa matsayin Turkiyya a matsayin karfin kariya da za ta iya samar da tsarin ga duniya.
Yayin da tsarin ke tafiya zuwa kasuwannin kasa da kasa, 'yancin kai a fannin fasaha na Turkiyya da dabarun yaki na zamani babu abin da zai ci gaba da yi sai bunkasa.

















