WASANNI
2 MINTI KARATU
Dan wasan PSG Mbappe ya ce ba zai tafi Real Madrid ba
Tun da farko jaridar Le Perisien ta kasar Faransa ta yi ikirarin cewa Mbappe zai tafi Real Madrid a bazara bayan Benzema ya bar PSG.
Dan wasan PSG Mbappe ya ce ba zai tafi Real Madrid ba
Mbappe  ya koma PSG ne daga Monaco a 2018 a yarjejeniyar dindindin bayan ya yi zaman aro a kungiyar na kakar wasa daya. Hoto/Getty / Others
14 Yuni 2023

Fitaccen dan wasan Paris Saint-Germain (PSG) Kylian Mbappe ranar Talata ya musanta rade-radin da ake yi cewa zai tafi Real Madrid a bazara.

"Karya ce... Wannan babbar karya ce. Tuni na ce zan ci gaba da murza leda a PSG a kakar wasa mai zuwa, inda na fi samun farin ciki," in ji Mbappe a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dan wasan gaban na Faransa Mbappe, mai shekara 24, ya koma PSG ne daga Monaco a 2018 a yarjejeniyar dindindin bayan ya yi zaman aro a kungiyar na kakar wasa daya.

A 2022, Mbappe ya tsawita yarjejeniyarsa a PSG zuwa 2025, a yayin da ake rade-radin cewa zai tafi Real Madrid a kakar wasa ta 2021-22.

Tun da farko jaridar Le Perisien ta kasar Faransa ta yi ikirarin cewa Mbappe zai tafi Real Madrid a bazara bayan Karim Benzema ya bar PSG.

A makon jiya, Benzema ya yi bankwana da Real Madrid inda ya tafi kungiyar kwallon kafar Al-Ittihad ta kasar Saudiyya.

Mbappe yana cikin manyan 'yan wasan Faransa da PSG domin kuwa ya taimaka wa kasar ta dauki Kofin Duniya na 2018.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda