TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai ya yaba da goyon bayan Turkiyya ga Ukraine a yaƙinta da Rasha
‘‘Turkiyya muhimmiyar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, kuma tana ba da gudumawa a koƙarin majalisar EU na ganin an sasanta,’’ a cewar Antonio Costa.
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai ya yaba da goyon bayan Turkiyya ga Ukraine a yaƙinta da Rasha
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Turai Antonio Costa da shugaban Turkiyya Recp Tayyip Erdogan / AA
15 awanni baya

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya yaba wa Turkiyya bisa rawar da take takawa wajen nuna goyon bayanta ga Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha a ganawar da ya yi da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya kan samar da ƙasashe biyu.

Costa ya faɗa a ranar Litinin cewa taron yana da ‘‘muhimmici’’ kuma "Turkiyya babbar abokiya ce da ke goyon bayan Ukraine, wadda ke ba da gudunmawa a ƙoƙarin majalisar EU na ganin an sasanta."

Ya ƙara da cewa EU za ta ci gaba da yin aiki tare ƙasar don samun "zaman lafiya mai ɗorewa."

‘‘A shirye mu ke don yin jagoranci a kowane yanki don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa’’

Taron ‘‘gamayyar ƙasashe da ke neman saulhu’’ da ya gudana kwanan baya a birnin Paris a ranar 4 ga watan Satumba ya ja hankali inda aka samar da sabbin alƙawuran tsaro ga Ukraine, yayin da yaƙin Rasha ke ci gaba da ɗaukar zafi.

Turkiyya wacce ke koƙarin tsayawa a tsakiya tsakanin Mosko da Kiev tun daga lokacin da aka soma yaƙin, ta jaddada buƙatarta na ganin an samar da zaman lafiya a taron.

Bayan taron, mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yılmaz ya bayyana cewa, ‘‘a shirye Ankara take ta jagoranci kowane fanni domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yaƙin Rasha da Ukraine.’’

A baya, Ankara ta karɓi baƙuncin wani taron tattaunawar kai-tsaye tsakanin jami'an Rasha da na Ukraine, kuma ta kasance babbar mai shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniyar cinikin hatsin da aka cim ma ta tekun Bahar Rum, wadda ake gani a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin diflomasiyya tun bayan ɓarkewar rikicin a shekarar 2022.