NIJERIYA
2 minti karatu
Dole ɗaliban Nijeriya su gabatar da kundin bincike na kammala karatu (Project) kafin NYSC - Gwamnati
Gwamnatin ƙasar ta ce daga ranar 6 ga Oktoba, babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince ya yi NYSC ko hutar da shi ba tare da bin tsarin NERD ba.
Dole ɗaliban Nijeriya su gabatar da kundin bincike na kammala karatu (Project) kafin NYSC - Gwamnati
Wannan umarni ba shafi masu yi wa ƙasa hidima ba waɗanda suka fara hidimar kafin a fitar da wannan sanarwar. / NYSC
29 Satumba 2025

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da bin ƙa’idojin Hukumar Tsare-Tsare ta Ilimi da Ajiyar Bayanai ta Nijeriya (NERD) a matsayin sharaɗi na tilas don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Ka’idojin sun tanadi cewa, daga ranar 6 ga Oktoba, babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince ya yi NYSC ko hutar da shi ba tare da bin tsarin NERD ba.

Sakataren Gwamnati Tarayya George Akume ne ya aika da wannan umarnin a cikin takarda ta musamman ga duka ma’aikatun gwamnatin ƙasar a ranar Lahadi a Abuja.

Sai dai wannan umarni ba zai shafi masu yi wa ƙasa hidima ba waɗanda suka fara hidimar ƙasar kafin a fitar da wannan sanarwar.

Akume ya bayyana cewa na bayar da wannan umarnin domin kawo gyara tsarin yadda ake kiran ɗalibai aikin yi wa ƙasa hidima daidai da ƙa’idojin da ofishin shugaban ƙasa ya fitar na yin ɗa’a ga hukumar NERD.

Daga cikin abubuwan da ake buƙata daga ɗaliban Nijeriya a wannan sabon tsarin har da abubuwan da suka gudanar a makarantunsu, daga ciki har da kundin bincike na kammala karatu wato project.