Yajin aikin da ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar ta Nijeriya (PENGASSAN) ta fara ranar Litinin ya katse aiki a mahimman ma’aikatu da hukumomi na fannin man fetur ciki har da kamfanin man Nijeriya NNPC da hukumomin da ke sa ido kan harkoki haƙowa da rabawa da kuma tace mai.
Yajin aikin, wanda ya biyo bayan umarnin kwamitin zartarwar ƙungiyar, ya sa mambobin ƙungiyar a fadin ƙasar sun ƙaurace wa aiki, lamarin da ya kulle mahimman ma’aikatu da hukumomin da ke jagorantar fannin man Nijeriya.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce hedikwatar hukumar NUPRC mai kula da haƙo mai a ƙasar ta kasance a kulle ranar Litinin, inda ma’aikata suka kasa iya shiga hedikwatar.
Jami’an tsaro da ke aiki sun tabbatar da cewa babu ma’aikacin da aka bai wa damar shiga, bisa umarnin ƙungiyar.
Kazalika, harkoki a hedikwatar hukumar NMDPRA mai kula da yadda ake dakon ɗanyen mai a tsakiyar Abuja inda ake yawan hada-hada sun tsaya cak saboda yajin aikin.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban PENGASSAN a hukumar NMDPRA, Tony Iziogba, ya bayyana cewa ƙungiyar ta yi nasarar tabbatar da aiwatar da yajin aikin 100 bisa 100, lamarin da ya hana ma’aikata da baƙi shiga ofishin.
Ya ƙara da cewa abokanan aikinsa sun tabbatar da cewa an bi umarnin yajin aikin 100 bisa 100 a hedikwatar kamfanin man Nijeriya NNPCL da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.
PENGASSAN ta ce yajin aikin ya zama dole ne bayan zargin da ta yi na kora ba bisa ƙa’ida ba da aka yi wa ma’aikata 800 a Matatar Man Dangote.
Umarnin ƙungiyar na dakatar da bayar da ɗanyen mai da iskar gas ga Matatar Man Dangote ya saka damuwa a fannin na makamashin Nijeriya inda kamfanonin da ake sayar da mai ke gargaɗin cewa za a samu tsaiko mai tsanani wajen samar da mai, lamarin da zai sa a ƙara farashin mai.