Yadda zabiya a Afirka ke shawo kan ƙalubalen rayuwa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Yadda zabiya a Afirka ke shawo kan ƙalubalen rayuwaBayanai sun nuna cewa mutum ɗaya cikin duk mutane 5,000 a Afirka kudu da Sahara, zabiya ne.
Mutane zabiya a bikin rawa da kwalliya na maza da mata a Afirka ta Kudu. / Hoto: AP
13 Yuni 2024

Daga Mazhun Idris

Ana kallon al'adar muzgunawa mutane zabiya a matsayi al'adar da wasu al'ummomi masu ci-baya ke yi, musamman a Afirka.

Sai dai kuma, akwai labarin wasu 'yan-biyu a Amurka da ake kira Muse Brothers, wanda labari ne da ba a yawan ba da shi.

George da Willie Muse wasu 'yan-biyu ne Amurkawa 'yan asalin Afirka, wanda suke zabiya ne.

An sace su tun suna yara a birnin Truevine na jihar Virginia a shekarar 1899, sannan aka ringa amfani da su a wasannin ba-da-dariya don biyan kuɗi, har zuwa shekarar 1927.

Daga haihuwa

'Yan biyun da aka bautar da su, sun sha wahala a hannun fararen fata waɗanda suka sace su, suke neman kuɗi da su, kuma suna kiran su da suna na ƙasƙanci.

Wannan ƙyama kan zabiya daɗaɗɗiya ce.

Kalmar zabiya a harsehn Ingilishi, wato "Albinism" an samo ta ne daga kalmar harshen Latin ta "albus" mai ma'anar "fari."

Ana samun yanayin zabiya ne tun daga haihuwa, kuma yana faruwa ne sakamakon ƙaranci ko rashin sinadarin melanin a jikin fata da gashi da idanu.

Haɗari

Wannan ne ke jawo wa zabiya faɗawa haɗarin tasirin zafin rana.

Bayanai sun nuna cewa mutum ɗaya cikin duk mutane 5,000 a Afirka Kudu da Hamadar Sahara, suna rayuwa da yanayin zabiya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce duk mutum ɗaya cikin mutane 20,000 a Turai da Kudancin Amurka yana da yanayin zabiya.

Donald Tampi Bagas wani ɗan Nijeriya ne wanda aka haifa zabiya. Rayuwarsa ta zabiya ba ita ce "ta dame shi ba", sama da matsalar rashin gani sosai da rana, da kuma ƙyama a wasu lokuta.

An haife shi a jihar Nasarawa da ke yankin tsakiyar Nijeriya. Iyayensa sun ba shi ƙwarin gwiwa a lokacin yarintarsa a shekarun 1980s da 1990s.

Tsananin haske

Donald wande ke da shekaru 35 ya shawo kan nuna ƙyama da ake masa saboda zamansa zabiya. A yanzu yana aiki a babban birnin Nijeriya, Abuja, tare da wata ƙungiya mai taimaka wa mutane da fama da nakasa.

A Zimbabwe, cikin duk mutane 1,000 akwai mutum guda zabiya, inda a Tanzania kuma cikin duk mutane 1,400 mutum guda zabiya ne.

A Afirka ta Kudu, cikin duk mutane 3,900 masu duhun fata, mutum guda zabiya ne.

Kusan duk mutanen da ke zabiya suna fama da matsalar gani, saboda tsananin haske yana cutar da su.

Aikin zahiri

Donald ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Hasken rana yana matsa min. Ba abin da zan iya yi don sauya wannan yanayi, don haka na koyi rayuwa da wannan yanayi".

"Lokacin ƙuruciyata, ba na son tsayuwar taron asambili saboda rana tana damu na ba na gani sosai."

Matsalar ganin tana kuma shafar ayyukansa na zahiri sanda yana ƙarami, kamar wasan ƙwallon ƙafa.

Ya tuna yadda yake a lokacin, "Ba na iya ganin abin da ke nesa. Wannan ya tilasta min zama a kujerar gaba a aji".

Wayar da kai

Donald ya ce ƙyama saboda dalilin zamowa zabiya, shi ya sa ya ke aiki da ƙungiya mai zaman kanta, ta TAF Africa, wadda ke wayar da kan mutane game da yanayin zabiya, kuma take neman shigo da su harkar tafiyar da al'umma.

A wasu ƙasashen, yawancin mutane zabiya suna mutuwa sakamakon cutar kyansar fata tsakanin shekaru 30 da 40, cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

TAF Africa ta taimaka wa Nijeriya wajen samar da tsare-tsaren ɗaukaka haƙƙoƙin mutane zabiya.

Donald ya ce, "A ayyukansu na yau-da-kullum, mutane zabiya suna shiga rana. Wasunsu ba su san yadda za su kare kansu daga zafin rana. Muna buƙatar ilmantar da mutane kan yadda za su kare lafiyarsu".

Al'umma na buƙatar ilmantarwa

Donald ya ƙara da cewa al'umma na buƙatar a ilmantarwa kan yadda za a yi mua'amala da mutane zabiya.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce nuna wariya ga mutane zabiya bai dace da kyawawan ɗabi'un ɗan-adam ba.

A wasu al'ummomi, mutane zabiya suna fuskantar tsangwama a zahiri, da ƙyama, a wasu lokuta har da kisa don yin tsafi.

Jake Epelle, shugaban ƙungiyar TAF Africa, ya yaba wa hukumar zaɓe ta Nijeriya saboda samar da gilashin ƙara girman rubutu a tashoshin zaɓe da aka yi a shekarar 2023, don taimaka wa mutane masu matsalar gani, cikinsu har da zabiya.

'Matsalolin zahiri'

Ana bikin Ranar Zabiya ta Duniya duk ranar 13 ga Yuni duk shekara.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu nasarori a zahirance a al'umma, amma ana buƙatar tabbatar da al'ummar zabiya su samu cikakken more rayuwa da haƙƙoƙinsu.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Fadan 'yan daba da gwamnati ya jawo asarar rayuka 1,200 a cikin wata uku a Haiti - MDD
Numfashi na mana wahala saboda gurbacewar iska a birnin New Delhi na India
An soke tashin jiragen sama fiye da 2,000 a Amurka yayin da harkokin gwamnati ke ci gaba da dagulewa
Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙi
COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi