Hukumar NBRDA mai kula da bincike da ci-gaban fasahar halittu ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya amincin abincin da aka sauya wa halitta (GMO) da kuma mahimmancinsu wajen magance matsalolin abinci na Nijeriya.
Babban daraktan NBRDA, Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce sau da yawa labaran ƙarya da tsoro na sa damuwa game da GMO, yana mai jaddada cewa hukumar tana ƙarfafa wayar da kan jama’a da hujja domin samar wa mutane ƙwarin gwiwa.
Ya bayyana cewa an yarda da abincin da aka sauya wa halitta (GMO) a duniya gabaɗaya a matsayin masu aminci kuma ana gudanar da bincike da tabbatar da tsari wajen amfani da su.
A Nijeriya, babu kaya na GMO da ake bai wa damar yawo ba tare da izini daga hukuma mai kula da tsaron halittu ta ƙasa (NBMA) bayan cikakken bincike kan barazanar.
Farfesa Mustapha ya bayyana mahimman alfanun GMO, ciki har da samun amfanin gona mai yawa da ingancin yaƙi da cututtuka da ragin amfani da sinadirai masu cutarwa da kuma ƙarin juriya kan sauyin yanayi— ababen da manoman Nijeriya suka fara morewa.
Ya jaddada cewa ilimin fasahar halittu na taimaka wa maimakon maye gurbin noma na al’ada, inda yake bai wa manoma kayayyakin aiki domin bunƙasa harkarsu da samunsu da ɗorewar aikinsu.
Shugaban na NBRDA ya jaddada jajircewar hukumar fayyace gaskiya ɗa’ar halittu da tsaron jama’a yayin da take inganta ilimin fasahar halittu domin inganta ci-gaban noma da tattalin arziƙi.