NIJERIYA
2 minti karatu
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban INEC
Farfesa Amupitan shi ne zai maye gurbin Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban INEC
Farfesa Joash Ojo Amupitan shi ne zai maye gurgin Mahmood Yakubu a shugabancin INEC bayan majalisar dattijai ta amince da shi / Public domain
9 Oktoba 2025

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, don maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, a cewar fadar shugaban ƙasa.

Wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Alhamis, ta ce Majalisar Magabatan Kasar ta amince da Farfesa Amupitan, bayan shugaba Tinubu ya miƙa sunansa.

“Shugaba Tinubu ya shaida wa Majalisar Magabatan cewa, Amupitan shi ne mutum na farko daga jihar Kogi da aka naɗa a matsayin shugaban INEC, sannan ba ɗan siyasa ba ne,” a cewar sanarwar ta Onanuga.

Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu zai miƙa sunan sabon shugaban ga Majalisar Dattijai domin amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Wane ne Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN)?

A ranar Talata ne tsohon shugaban hukumar Mahmood Yakubu ya bar ofis inda ya tafi hutun ƙarshen aiki, yayin da wata biyu ya rage cika shekaru goma cif yana jagorantar hukumar zaɓen ta ƙasa.

Sabon shugaban na INEC mai shekaru 58 a duniya, farfesa ne a ɓangaren koyar da aikin shari’a, wanda ke koyarwa a Jami’ar Jos da ke jihar Filato.

Ɗan asalin jihar Kogi, Amopitan ya fara aikin lauya a 1988 bayan kammala digiri a Jami’ar ta Jos. Ya zama babban lauya na Nijeriya mai mukamin SAN a Satumbar 2014.

Ya yi aikin hidimar ƙasa NYSC a jihar Bauchi, kamar yadda sanarwar Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana.