NIJERIYA
4 minti karatu
Mutum 26 da ake zargi da garkuwa da mutane sun shiga hannun ‘yan sanda a Kaduna
Kamen ya biyo bayan wasu samamen da jami’an ‘yan sandan da ‘yan sa kai suka kai tsakanin 3 da 5 ga watan Oktoba na shekarar 2025, inda suka mayar da hankali kan  ƙungiyoyin da ke aika-aika a ƙananan hukumomin Anchau da Ikara da kuma Makarfi.
Mutum 26 da ake zargi da garkuwa da mutane sun shiga hannun ‘yan sanda a Kaduna
Ana yawan samun matsalar garkuwa da mutane a arewacin Nijeriya / AP
13 awanni baya

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargi da garkuwa da mutane kuma ta ƙwace bindigogi huɗu da aka ƙera da kuma wasu muggan makamai da kuma wani kaso na kuɗin fansa da aka biya su a garkuwa da mutane a wurare daban daban a faɗin jihar.

Kamen ya biyo bayan wasu samamen da jami’an ‘yan sandan da ‘yan sa kai suka kai tsakanin 3 da 5 ga watan Oktoba na shekarar 2025, inda suka mayar da hankali kan  ƙungiyoyin da ke aika-aika a ƙananan hukumomin Anchau da Ikara da kuma Makarfi.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan a ranar Alhamis ya bayyana cewa, aikin da aka aiwatar da haɗin gwiwar hukumar ‘yan bijilanti ta Kaduna, wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi domin kawar da fashi da garkuwa da mutane daga jihar.

Sanarwar ta ce nasarar ta farko ta samu ne a ranar 5 ga watan a lokacin da tawagar ‘yan sintirin daga rundunar ‘yan sandan da ke Anchau, wadda ta yi aiki kan bayanai na sirri, ta  kutsa maɓuyar masu garkuwa da mutane da misalin ƙarfe 1:15 na dare kuma suka kama mutum shida da ake zargi, ciki har da mai suna Jibrin Abubakar, wanda ake ce wa Oga, mai shekarar 21.

“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar 2025, wajen yin garkuwa da wani mai suna Idris Adamu, mai shekaru 60, wanda suka riƙe na tsawon kwanaki kafin su sake shi bayan sun karɓi kuɗin fansa na naira miliyan biyar,” a cewar Hassan.

A lokacin samamen, mutum biyu da ake zargi da aka bayyana sunayensu da Yunusa Iliya (mai shekarar 31) da Malam Iliya (mai shekara 55), daga ƙauyen Gidan Sidi a gundumar Anchau, an kama su ne bayan wata musayar wuta ta ƙanƙanin lokaci da ‘yan sanda. Wasu mutum biyu kuma sun samu sun tsere kuma a halin yanzu inda jami’ai ke neman su.

Ababen da aka ƙwace daga waɗanda ake zargin sun haɗa da bindigogi ƙirar Pump Action da aka ƙera a gida guda biyu da fankon gidajen harsasai biyar da wasu layu da kuɗi N546,000, wanda aka yi imanin cewa wani ɓangare ne kuɗin fansa da iyalan waɗanda aka kama suka biya.

A wani aikin na daban kuma ranar 3 ga watan Oktoba, jami’an rundunar da ke yaƙi da garkuwa da mutane sun kama wani mai suna Habibu Alhaji Ahmadu, da aka fi sani da suna Munyaye, a ƙramar hukumar Ikara.

Wanda ake zargin, wanda aka samu da bindigogi biyu da aka ƙera a gida, ya amsa kitsa wani hari na fashi da makamai a gidan wani ɗan kasuwa a yankin.

“Bincike na farko ya nuna cewa Ahmadu wani mamba ne na wata ƙungiya da ta addabi Ikara da kewaye. Yana aiki ne da abokan aikata lafinsa da aka bayyana sunayensu a matsayin Buhari da Shede, wanda a halin yanzu ana neman su,” a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan.

Ya ce a halin yanzu ana ƙoƙarin nemo inda suke tare da karɓe makaman da ke hannayensu da ƙungiyar ke amfaniu da su wajen aika-aika.

Wata muhimmiyar nasara kuma ta zo a ranar 4 ga watan Oktoba a lokacin da jami’ai da ke aiki kan bayanan sirrin waɗanda aka yi garkuwa da su kwanan nan suka bayar, suka far ma maɓuyar masu garkuwa da mutane a ƙauyen Gazara, da ke Ƙaramar Hukumar Makarfi.

A lokacin samamen, waɗanda ake zargi 14 ciki har da wani mai suna Bello Umar, wanda aka taɓa tuhuma da garkuwa da mutane suna shiga hannu. ‘Yan sanda sun kuma ƙwace adduna da kuma sauran makamai masu hatsari daga wurin.

Hassan ya ce daga baya an kama rin waɗanda ake zargi a yankin Toll waɗada ke da alaƙa da gungun masu aikata laifin.