NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kuɓutar da mutane 37 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ‘yan ta’adda 9
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa haɗakar sojojin ƙasa na Nijeriya da wasu dakarun ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda tara, tare da kama mutum 8 da ake zargi da laifuka, da ƙwato manyan makamai.
Sojojin Nijeriya sun kuɓutar da mutane 37 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ‘yan ta’adda 9
A wani samame daban a iyakar Ekiti da Kogi, sojojin bataliya ta 148 sun kashe ‘yan ta’adda biyu / Reuters
9 Oktoba 2025

Sojojin Nijeriya sun kuɓutar da mutum 37 da aka yi garkuwa da su, a wani samame na musamman na yaƙi da ta’addanci da satar mutane a faɗin ƙasar tsakanin 2 zuwa 6 ga Oktoban 2025.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa haɗakar sojojin ƙasa na Nijeriya da wasu dakarun ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda tara, tare da kama mutum 8 da ake zargi da laifuka, tare da ƙwato manyan makamai.

A yankin Arewa maso Gabas, sojojin bataliya ta 151 Task Force sun yi kwanton-ɓauna ga ‘yan ta’addan ISWAP da Boko Haram a kusa da garin Dipchari a Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno, inda suka kashe ‘yan ta’addan biyar a abin da aka bayyana a matsayin “gagarumar musayar wuta.”

“A wani samame daban a iyakar Ekiti da Kogi, sojojin bataliya ta 148 sun kashe ‘yan ta’adda biyu, tare da ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47.

“Haka kuma, bataliya ta 3 ta daƙile wani hari mai girma da aka kai mata, inda ta jikkata da dama daga cikin maharan inda ta kashe ɗaya daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga.

 “A jihohi da dama ciki har da Borno, Katsina, Imo, da Filato, sojoji sun kama mutane takwas da ake zargi da hannu a ta’addanci, satar mutane, da safarar makamai.

“Cikin waɗanda aka kama akwai wani da ake zargi da kasancewa mai kai wa ISWAP kaya a Monguno, wani abokin hulɗar ‘yan ta’adda a Kukawa, wani jami’in ƙungiyar ‘yan a-ware IPOB/ESN a Imo da kuma wani mai safarar makamai a Jihar Filato.

“Sojoji sun kuma ƙwato makamai da dama ciki har da ƙaramar bindiga ƙirar gida, da harba-ruga ɗaya, kurtunu na AK-47 ɗauke da alburusai fiye da 100 iri daban-daban, da kuma babura da dama da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka.”