Gwamnatin Nijeriya ta musanta rahoton da Bankin Duniya ya fitar wanda ya yi ƙiyasin cewa ‘yan ƙasar miliyan 139 suna rayuwa cikin talauci, tana mai cewa ya ci karo da hankali kuma ya saɓa wa yanayin tattalin arzikin ƙasar.
Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan watsa labarai, Sunday Dare, ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba cewa ƙididdigar da Bankin ya yi amfani da ita wajen fitar da rahoton ba ta yi la’akari da wasu bayanai masu muhimmanci da ke taimaka wa ci-gaban ƙasa ba.
“Duk da cewa Nijeriya tana martaba haɗin gwiwarta da Bankin Duniya kuma tana jin daɗin gudunmawar da yake bayarwa kan manufofinta, dole a sanya alƙaluman da aka ambato cikin yanayi da ya dace,” in ji Dare.
Fadar gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa adadin mutum miliyan 139 da rahoton ya ambato an samo shi ne bisa ma’aunin talauci na duniya kan $2.15 ga ko wane mutum ɗaya a yini wanda aka tsara a shekarar 2017, kuma bai kamata a yi amfani da shi wajen ƙirga adadin talakawa a Nijeriya ba.
Sunday Dare ya bayyana cewa idan aka sauya kuɗin zuwa naira kuma aka yi lissafa $2.15 zuwa kwana talatin, za ta kai $64.5, wato tana daidai da kimanin naira 100,000, kuɗin da ya zarta albashi mafi ƙanƙanta a Nijeriya naira N70,000.
“Dole a yi taka-tsan-tsan wajen fassara alƙaluman Bankin Duniya kai-tsaye,” in ji shi.
“An samo ƙiyasin ne daga ma’aunin talauci na duniya na $2.15 ga ko wane mutum, ƙiyashin da aka tsara a shekarar 2017,” in ji Dare.
Ya ƙara da cewa auna talauci bisa tsarin ƙimar kuɗi da bankin ya yi amfani da shi yana amfani ne da alƙaluman tarihin yadda ake kashe kuɗi (a shekarun 2028/19 ne Nijeriya ta tattara irin waɗannan bayanan) kuma yawanci ba ya mayar da hankali kan hada-hadar kuɗi na tsarin kan titi da na kamfanoni wanda a kansa ne miliyoyin iyalai suka dogara.
Saboda haka gwamnatin tana ganin alƙaluman sun bi ƙiyasin duniya ne, maimakon bayyana haƙiƙanin halin da ake ciki a Nijeriya a shekarar 2025 a cewar Sunday Dare.